Tatsuniya a Ƙarƙashin Tsamiya
Muna masu matuƙar farin cikin fara gabatar muku da jeremgiyar littafan tatsuniya wanda aka yiwa taken: Tatsuniya a Ƙarƙashin Tsamiya. Littafai ne guda huɗu wanda kowannensu ya ke ɗauke da tatsuniyoyi da labaru har guda hamsin da ɗaya. An tsara labarun ne domin su dace da gyaran tarbiyyar yara da ma matasan wannan zamani da kuma kaifafa musu basira ta inda za su ƙara sha'awar karantawa da kuma koyon yanda ake rubuta ƙirƙirarrun labarai a harshen mu na Hausa mai albarka. A tsarin waɗannan littafai wata tsohuwa ce mai suna Iyata wadda ta ke baiwa yara tatsuniyoyi da waƙoki da hikayoyi a ƙarƙashin wata tsohuwar bishiyar Tsamiya wadda duk mutanen garin su ma tasowa su ka yi su ka ganta. A bisa tsarin wannan tsohuwa wato Iyata mai Tastuniya, kowane yaro sai ya kawo wasu ƴan kuɗaɗe kafin ya zama ɗaya daga cikin masu sauron tatsuniyoyinta a kowane dare. Ita kuma da ƴan waɗannan kwabbai ne ta ke sam...