Posts

Showing posts from July, 2022

Ga ta Nan Ga ta Nan ku

Image
Gata nan kuma gata nan ku Kunnuwa ne gareku? To azo wasu kan na naku Sai ku karkaɗe kunnuwanku Hankalanku ku ban aro ku Gayyato mini ƴan uwanku Ni Iyanku ina gaban ku Ƴar Gizo na tawo na baku Duk cikin zan gargaɗe ku Zani wanke zuciyar ku Za su sauya baƙin halinku Kwai fa labarin gaban ku Don ku rayu a duniyar ku Har ku tsira a lahirar ku Ga dabaru sai ku ɗauku Duk yawan ƙaryar Gizon ku Ƙoƙi mai haƙuri ta ganku Ga halin namun dawan ku Don ku ɗau darusa a ran ku Kar ku mance zubin garinku Har ku ɗauki halin wasun ku Ƙarƙashin daɗa tsamiyar ku Zan zubo muku kui shirun ku Sai ku tattara ƴan kuɗin ku Don ku ƙarfafi gyatumar ku Mai biɗar gyaran halin ku Kar ku ce na gundure ku To ƙurunƙus za ni bar ku Na yi ƙarya don gizon ku Ga fa ɓera nan gaban ku In ka tsorata alhakin ku Ba ruwan iya gyarumar ku