Ga ta Nan Ga ta Nan ku
Gata nan kuma gata nan ku
Kunnuwa ne gareku?
To azo wasu kan na naku
Sai ku karkaɗe kunnuwanku
Hankalanku ku ban aro ku
Gayyato mini ƴan uwanku
Ni Iyanku ina gaban ku
Ƴar Gizo na tawo na baku
Duk cikin zan gargaɗe ku
Zani wanke zuciyar ku
Za su sauya baƙin halinku
Kwai fa labarin gaban ku
Don ku rayu a duniyar ku
Har ku tsira a lahirar ku
Ga dabaru sai ku ɗauku
Duk yawan ƙaryar Gizon ku
Ƙoƙi mai haƙuri ta ganku
Ga halin namun dawan ku
Don ku ɗau darusa a ran ku
Kar ku mance zubin garinku
Har ku ɗauki halin wasun ku
Ƙarƙashin daɗa tsamiyar ku
Zan zubo muku kui shirun ku
Sai ku tattara ƴan kuɗin ku
Don ku ƙarfafi gyatumar ku
Mai biɗar gyaran halin ku
Kar ku ce na gundure ku
To ƙurunƙus za ni bar ku
Na yi ƙarya don gizon ku
Ga fa ɓera nan gaban ku
In ka tsorata alhakin ku
Ba ruwan iya gyarumar ku
Comments
Post a Comment