ƳAR BORA DA KIFANYA
YAR BORA DA KIFANYA
Wata yarinya ce ta taso a gidan da aka mayar da mahaifiyarta bora, duk wani aikin wahala na gidan da ita da mahaifiyarta ne su ke yin sa ga tsamgwama.ga kuma makirci. Yayinda ita kuma Mowaa da ƴaƴanta suna kwance ma ake kai musu abinci bayan an gama.
Ana cikin wannan hali, wata rana sai mai gidan ya sayo kifaye daga wajen masu su mai tarin yawa. Ya na kawowa ya ajiye sai Mowa ta ce da ƴar bora cikin isa da mallaƙa "Ɗauki kifayen nan ki je rafi ki wanko mana su tatas kuma na riga na ƙirga su, idan na ga babu guda ɗaya sai na lahira ya fi ki jin daɗi" Kasancewar lokacin ɗari ne, Jikin yarinya na karkarwar saboda ɗari da kuma ta tsoron faɗan maƙetaciyar kishiyar mahaifiyarya, ta ɗebi kifi ta tafi rafi.
Ta na cikin wanke kifi ne kawai sai ta ga guda ɗaya ta tashi da rai har ta na yi mata magana ta na cewa " Ƴarinya ki dubi Allah ki bar ni na je na shayar da ariraina a cikin ruwa amma na yi miki alƙaearin zan komo" Yarinyar ta saki kifanya a ckin ruwa. Jim kaɗan kafin ta ƙarasa wanke sauran kifayen sai ga kifanya ta komo cikin hanzari. Yarinya ta ce da kifanya "Je ki abin ki ki kula da jariranki. Kifanya ta ce: "Aa na san an sai an doke ki a gida ai" Yarinya ta ce " Kawai ki yi tafiyar ki abinki.
Bayan yarinya ta koma gida aka ƙirga kifaye aka ga babu wannan babbar sai fa aka dinga zaginta da duka har sai da mahaiginta ya ce a bari idan ya je kasuwa zai ƙaro wani sannan aka ƙyaleta.
Washegari yarinya ta je ɗebar ruwa a rafi sai kifanya ta taro duk ƴan uwanta ta ce musu su zo su ga yarinyar da ta yi mata rai. Nan fa duk su ka taru ana ta yi mata godiya. Kifanyar ta ce da ita " Na ji cewar a lokutan bikin sallah Sarki ya shirya gagarumin wasa a gidan sa ko?" Yarinya ta ce "e haka ne" Sai kifanya ta ce to idan za ki je ki biyo ta nan kafin ki wuce can.
Da ranar wasan sallah ta zo aka ɗauko gyauto da mayafai masu tsada aka baiwa ƴaƴan Mowa, amma ita yarinya aka ɗauko wani tsumman gyauto duk jikn sa yaga aka bata ta ɗaura ko mayafi ma baɓu. Haka nan yarinya ta yi ɗaurin ƙirji ta tafi rafi wajen kifanya. Kifanya ta ɗauko wata taskira ta bata. Sai ga kayan ado iri-iri, na tufafi da tsakiyoyi da awarwaro da munduwa duk na zinare da azurfa. Sannan kuma sai kifanya ta feso mata ruwan da ta guntso a bakinta sai ga yar bora ta ƙara kyau ta yi jajur kamar tsada, kuma gashinta ya na sauka baya kamar zai ja kasa.
Da yarinya ta je wajen wasan sallah a gidan Sarki sai kuwa idanun Sarki su ka kai kanta, Sarki ya na dinga kallontanhar har yawu yana dalala daga bakinsa.
Anan take dai Sarki ya ce ya na neman aurenta ita kuwa yarinya ta ce: "Ai.ba a wajen wasa aka haife ni ba da za'a nemi aurena anan." Sai Sarkin ya aika tawaga da kyautuka na ƙasaita zuwa mahaifinta da kuma sanarwar cewa ya ga ƴar sa ya na son ta da aure. Nan fa Mowa ta fito kamar ta yi hauka ta na cewa sam wai ba nan gidan ba ne. Bayan tawagar Sarki sun tabbatar da cewa nan gidan ne kuma su ka nuna ƴar bora su ke ce ita ce wadda Sarki ya gani, sai mahaifinta ya yi murna ƙwarai kuma ya amince. Aka sha ƙasaitaccen bikin da ba'a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa.
Kafin a kai ta gidan Sarki, sai yarinya ta je ta yi sallama da kifaye kuma su ka ce idan ta na da buƙatar wani ta sanar da su ko yaushe su a shirye su ke domin agaza mata.
Bayan an kai yarinya gidan miji sai kishiyoyi su ka ga kyawunta a lokacin da Sarkin ya tara su domin neman haɗin kai da kuma gabatar da juna. Ashe su duk ƙyashi mai tsanani ya kama su da kuma tsoron cewa wannan kyakkyawar yarinyar za ta iya ƙwace musu fada a wajen Sarki. Sai su ka haɗu su ka datse mata hannunta guda ɗaya kuma su ka dinga yaɗa cewa amaryar Sarki hannu ɗaya ne da ita.
A cikin dare yarinya ta aika wata kuyangarta can rafi wajen kifaye domin sanar musu halin da ake ciki. Ai kuwa tare da ƴar aiken ma su ka tawo suna cewa "Tunda ba ta bar mu mun yi kuka ba to mu ma ba za mu taɓa barin ta ta yi shi ba" A daren suka ɗauki hannun nan da aka datse su ka haɗa da dungulmin su ka mayar su ka shafe ko alamar rauni ba mai iya gani. Yarinya ta na yi musu godiya su ma su na yi mata godiya.
Da gari ya waye sai sauran matan Sarki su ka ɗebo hatsi su ka zuba a ƙaton turmin tsakar gida su ka ce yai lugude za ayi sabida murnar auren da Sarki ya yi don haka duk sauran kuyangi masu hidimar gida su fifo su kalli shagalin matan Sarki. Kafin hakan kuwa duk sun bi sun yaɗa cewa amaryar Sarki fa hannu ɗaya gareta.
Aka kira amarya cewa ta zo an fara lugude ta na fitowa sai aka ganta da hannaye biyu cikakku kuma har ta ɗauki taɓarya ita ma ta shiga cikin ƴan lugude. A nan ne fa duk sauran matan Sarki su ka ji kunyar ƙaryar da su ka dinga yaɗwa domin kuwa jama'ar fada duk sai tsegungumi su ke yi kan batun su na zunɗen su. Haka nan amaryar Sarki ta cigaba da zamaanta cikin jin daɗi da farin ciki.
Ƙurunƙus!
Comments
Post a Comment