Saƙa Da Zare Ɗaya
Saƙa da Zare Ɗaya
A tsohon birnin Kano, a wata unguwa da ƙarar shurin masaka da karafniyar allira ke tashi dare da rana, an yi wani matashi mai suna Bashir. Yana da burin ya zama gwani a harkar saƙar da ya taso yaga mutanen yankim duk suna yi. Yana son zama.cikakkem ƙwararre kamar malaminsa, Alhaji Tanko, wanda hannunsa ya shahara wajen fitar da zane mai kyau a jikin manyan riguna. Bashir ya fara koyon aikin da hanzari da kazar-kazar, amma bayan wasu watanni, sai ya fara karaya.
A duk lokacin da ya kalli babban aikin da ke gabansa—yadda zai haɗa zare kala-kala, ya tsara zane, ya kuma saƙa babban gyauto.mai.ɗauke da.launuka daban-daban—sai ya ji zuciyarsa gaba ɗaya ta karaya. Yana ganin dai aikin ya fi ƙarfinsa, kuma.sam.ba zai taɓa ƙwarewa ba. Aikin yana tafiya a hankali, kuma sau da yawa yakan yi kuskuren sai an warware duk nisan da.aka yi kuwa. Wannan abu yana matuƙar bashi taƙaici. Wata rana, cikin tsananin fidda rai, ya jefar da abin da yake kan saƙawa a ƙasa ya ce wa malaminsa, "Malam, ni dai wallahi na gaji. Wannan aikin ba irin nawa ba ne. Ya fi ƙarfina!"
Malam Tanko, wanda ya sha ganin irin wannan hali daga masu koyo, ya kalle shi a sanyaye. Bai ce komai ba. Ya tashi a hankali, ya ɗauko zare guda ɗaya, siriri, wanda da kyar ake iya ma ganinsa saɓoda siranta. Ya miƙa wa Bashir. Ya ce masa:!"Riƙe," Cikinndakakkiƴar murya ya ce masa "Ka tsinka shi yanzu yanzun nan."
Bashir ya kalli zaren, sannan ya kalli malaminsa cike da mamaki, yana.kallonsa galala kamar wani gaula. Ya karɓa dai, kuma da yatsunsa biyu kacal, ya tsinka shi ba tare da wata wahala ba. "Gashi nan, na tsinka," ya faɗa kamar yana son ya nuna cewa wannan wani aikin banza ne.
Malam Tanko ya gyada kai. Ya ve masa: "Madalla,". Daga nan, ya je inda ya ajiye wasu zarurrukan da yawa, ya haɗa su wuri guda, ya murɗe su suka zama tamkar igiya mai kauri da ƙwari. Ya sake miƙa wa Bashir. "Yanzu kuma, tsinka wannan mu.gani."
Bashir ya karɓi turfkarar zaren nan wannan karon da hannu biyu. Ya ja da dukkan ƙarfinsa, fuskarsa ta yi ja, wasu jijiyoyi suka fito a wuyansa zara-zara sun cika da jini. Ya sake gwadawa, ya ɗan karkace yana jijjiga jiki, amma ko gezau, tufkar zaren nan ba ta yi ba. Ko alama ya kasa tsinka ta. Cikin kunya ya ɗago kai ya kalli malaminsa. "Malam, wannan ya fi ƙarfina."
A lokacin ne Malam Tanko ya yi murmushi mai ma'ana. Ya ce, "Bashir, wannan tufkar zare ita ce babban riga da kake son ka saƙa. Zaren guda ɗaya da ka tsinka cikin sauƙi da farko kuwa, shi ne aikin yau da kullum da kake yi. Babu wanda zai iya saƙa babban riga a rana ɗaya, kamar yadda ba ka iya tsinka wannan tufkar ba. Amma kowa zai iya saƙa zare ɗaya a lokaci guda. Idan ka haɗa aikin yau da na gobe, da na jibi, dana gata dana citta….., sai duk zarurruka da daman da ka saƙa ɗaya bayan ɗayai, su haɗu waje guda su zama babban riga mai ƙwari kuma mai kyau wacce babu wanda zai iya yaga ta cikin sauƙi."
Wannan maganar ta ratsa zuciyar Bashir. Ya fahimci darasin nan take. Babban aiki ba a fara shi da girma. Ana farawa da zare ɗaya ne, da aiki kaɗan-kaɗan, har ya taru ya zama babban wani abin alfahari. Daga wannan rana, Bashir ya koma kan aikinsa da sabon salo, yana mai da hankali kan zare ɗaya a lokaci guda, kuma bai sake karaya ba.
A rayuwarku, wane babban aiki kuke jin tsoron farawa don kuna ganin girmansa? Shin kun taɓa fara wani abu kaɗan-kaɗan har ya zama babbar nasara daga bisani?

Comments
Post a Comment