Posts

Showing posts from September, 2025

Saƙa Da Zare Ɗaya

Image
Saƙa da Zare Ɗaya A tsohon birnin Kano, a wata unguwa da ƙarar shurin masaka da karafniyar allira ke tashi dare da rana, an yi wani matashi mai suna Bashir. Yana da burin ya zama gwani a harkar saƙar da ya taso yaga mutanen yankim duk suna yi. Yana son zama.cikakkem ƙwararre kamar malaminsa, Alhaji Tanko, wanda hannunsa ya shahara wajen fitar da zane mai kyau a jikin manyan riguna. Bashir ya fara koyon aikin da hanzari da kazar-kazar, amma bayan wasu watanni, sai ya fara karaya. A duk lokacin da ya kalli babban aikin da ke gabansa—yadda zai haɗa zare kala-kala, ya tsara zane, ya kuma saƙa babban gyauto.mai.ɗauke da.launuka daban-daban—sai ya ji zuciyarsa gaba ɗaya ta karaya. Yana ganin dai aikin ya fi ƙarfinsa, kuma.sam.ba zai taɓa ƙwarewa ba. Aikin yana tafiya a hankali, kuma sau da yawa yakan yi kuskuren sai an warware duk nisan da.aka yi kuwa. Wannan abu yana matuƙar bashi taƙaici. Wata rana, cikin tsananin fidda rai, ya jefar da abin da yake kan saƙawa a ƙasa ya ce wa malaminsa, ...