AUDU MAƘERI

AUDU MAƘERI

Ƙira wata babbar sana'a ce da aka gada tun kaka da kakanni. Gidan su Audu ya kasance ɗaya daga cikin mashahuran gidajen da su ka shahara da ƙira. Wannan ya sanya ma daga cikin ahalinsu ne ake naɗa sarkin ƙira na garin.
Su na da maƙeran fari da kuma na baƙi duk a cikin su.

Tun Audu ya na ƙarami aka gano cewa ya na da hazaƙa da baiwa ta musamman akan wannan sana'a. Ya kan ƙirƙiri abubuwa waɗanda ba'a saba yin su ba. A sanadiyyarsa aka samu sabbin abubuwa masu ban sha'awa da ƙayatarwa. Ya kasance ya iya duk ɓangarorin ƙira wato na maƙeran fari da na baƙi.

Idan aka tashi yin biki ko suna a gidan su kuwa, baƙi daga sauran maƙotan ƙashe ma su na shigowa domin kashe kwarkwatar idanuwan su da yanda ake wasannin al'adu na maƙera masu ƙayatarwa da ban al'ajabi. Idan aka haifi jariri kuma, sai an sanya shi a cikin huta an cigaba da hurata da zuga-zugi da ta yi jajur sannan a ciro ƙarfen da yayi jajur a cikin wuta a ɗoɗana masa amma ƴan kallo na gani ko gezau ba abinda ya same shi. Irin waɗannan abubuwan al'ajabi su sha faruwa akan idanun ƴan kallo. Wannan bukukuwan sun ƙarawa gidan su Audu Maƙeri suna da ƙima a idon sauran jama'ar ƙasar da ma.na maƙotan ƙasashe baki ɗaya.

Audu Maƙeri na ɗaya daga cikin maƙeran da su ka ƙera masun Nawata da Gawata mashahuran sarakunan nan na Kano shekaru sama da ɗari tara da su ka shuɗe, kuma shi ne ya haɗe su waje guda su ka samar da Tagwayen Masu da duk sarakunan Kano ke tunƙawo da su har zuwa rana mai kamar ta yau.
Shi dai wannan mashahurin maƙeri shi ne wanda ake faɗar sa a cikin wata sananniyar waƙar wasannan na gadon gadon da ake cewa Tsakani tsakani..... Inda a ƙarshe a ke cewa: 'A ina wutar ta faɗa? A gidan Audu Maƙeri'


Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya