AWAISU YARON KIRKI

AWAISU ƊAN ALBARKA

Yaron Kirki wato Awaisu yaro ne mai ladabi da biyya tun tasowar sa. Mahaifiƴar sa ce ta sanya masa wannan suna Ɗan albarka saboda bai taɓa saɓa mata ko janyo mata zagi ko abin faɗa a maƙota ba. Yaron kirki ya kasance abin kwatancen iyaye ga ƴaƴan su idan  su na yi musu gargaɗi ko nasiha.

Kullum mahaifiyar sa tana yawan yi masa fatan alheri da addu'oin Allah ya ɗaukaka shi. Bayan ya cika shekara goma sha biyu ne ya fara bin fatake zuwa Agadas domin sayo kayan can da kuma kai musu kayan mu na nan ƙasar kamar kayan saƙi da kayan da maƙera su ka ƙera masu ban sha'awa. A hanyar su su kan gamu da ɓarayi da sauran namun dawa masu hatsarin gaske.

Yaron kirki ya kasance ba ya jin ko ɗar ko gezau ƙasancewar ya yi amanna da cewa babu wani mummunan abu da ya isa ya cutar da shi tunda dai ya na tare da addu'a da sanya albarkar mahaifiyar sa. Duk sanda za'a tafi fatauci sai an sanya shi ya jagoranci addu'a domin samun nasara da kuma neman tsari.

 Ana haka ne bayan ya cika shekara biyar da fara bin fatake wato lokacin ya shiga shekara ta sha bakwai sai su ka zo wucewa da wani daji mai surƙukin duhuwa. Kwatsan sai ga wata tawagar ƴan fashin daji duk sun rufe fuskokikln su da baƙaƙen kyallaye. Kowanne ɗaya daga ckin su na riƙe da muggan makamai wasu ma ba wanda ya taɓa ganin irn su ballantana ma ya yi ƙoƙarin yi musu suna.

Duk sai da kowa ya razana a cikimnayarin nan amma banda Awaisu Yaron Kirki. Awaisu ya ɗaga hannunsa sama ya roƙi Allah da wata irin murya madaidaiciya tsakanin bayyanawa da sirarrantawa. Nan take sai ga wani irin baƙin hadari mai haɗe da ƙura irin ta hamada ya turnuƙe sama. Iska na ɗiban duk abinda ta tarar a gabanta tana yin sama da shi. A gaban su su ka ga yanda guguwar nan ta tarkata ɓarayin nan ta yi sama da su tana murginawa da ƙara yin sama. Bayan ƙura ta lafa sai aka ga Awaisu a tsaye kyam hannunsa a ɗage zuwa sama ya na ta addu'a. Cikin wani abin al'ajabi tufafin kowa ya kyakkece ya yi buɗu-buɗu da ƙuta kamar waɗanda aka tono daga rami amma banda Awaisu. Shi nasa kayan ma kamar ƙara kyau da haske su ka yi.

Tun daga wannan ranar ne tawaga idan dai babu Awaisu a cikinta, to ba kowa ne ma ya ke son ya bi ta zuwa fatauci ba. Bayan da aka koma gida ne aka kwashe labari gaba ɗaya aka faɗawa sarki. Sarki ya tara manyan malamai ƙarƙashin babban limamin kofar fada aka kira Awaisu domim amsa tambayoyi bisa abinda ya aikata wanda ya ɗaurewa mutane kai. Wasu na cewa ai wannan ƙulumboto ne da surkulle wasu kuma na cewa ai karama ce ba yanda Allah ba iya ba..

Bayan malamai sun gama yi masa tambayoyi sai Babban Liman yace mahaifiyar sa tana nan a raye? Aka ce ma sa eh ta na nan da rai. Sai ya kuma cewa:: "To yaya danganta ka ta ke tsakanim su?" Aka bayyana masa cewa ai kullum sai ta sanya masa albarka da kyawawan fata saboda yanda ya ke kula da ita da yi mata biyayya. "Wannan ne ne! Wannan nan ne sirrin wannan yaron!" Liman  ya vigaba da faɗa ya nana yaro Awaisu da hannu cikin wani irin shauƙi mai kama da sanbatu.

Laman ya ƙara bayyana cewa: "Ai Waliyyin Allah Uwaisu ma da haka ya sami wannan matsayin na sa, inda har sai da ya kai sahabban Annabi ASW ma sai da Annabin ya ba su wasiyyar cewa duk sanda su ka gamu da shi su neme shi da ya yi musu addu'a. Hakan aka yi kuwa lokacin da Sayyidina Umar ya samu ƙaɓarin vewa Uwaisu ya zo aikin hajji a wata shekara lokacin ya na kan halifanci."

Liman nan take ya cire rawaninsa ya ce lallai sai Awaisu ya yi masa addu'a. Haka nan dai yaro Awaisu cikin jin kunya ya dafa kan Babban Liman ya yi masa wata addu'a mai tsayi. Bayan ya gama ne Laman ya yi ta yi masa  godiya cikin martabawa.

Daga wanan lokacin duk yaran garin kowa ya koma biyayya da jin maganar iyaye saboda kowa so ya ke shi ma ya zama abin sha'awa kamar yanda Awaisu Yaron Kirki.
 Ya zama har a fada ma ya na da mazauni na musamman saboda girmama shin da sarki ya ke yi.

Ƙurunƙus!

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya