BAREWA DA RAƘUMIN DAWA
BAREWA DA RAKUMIN DAWA
Wata rana barewa ta na cikin kiwo sai ta hango rakumin dawa a gabar kogi ya samu ciyawa sharshar ya na ta kiwo abinsa.
Barewa ta daga murya ta ce wa rakumin dawa: Ta ina ka wuce ka je gabar kogin nan? Rakumin dawa shi ma ya dago murya ya ce: Ta cikin ruwan mana. Har zuwa ina ruwan ya kawo maka? Barewa ta sake tambayar rakumin dawa. Iya kaurina. Rakumin dawa ya maido mata da jawabi. Rufe bakn sa ke da wuya sai barewa ta tsoma kafunta cikin ruwa ta hau linkaya. Ashe ruwan ba karamin zurfi ne da shi ba. Nan da nan ruwa ya nemi shanye kan barewa tana kuka ta na linkaya domin ganin ta tseratar da rayuwarta, har zuwa lokacin da Allah ya taimaketa dai igiyar ruwa ta ja ta zuwa gabar kogi.
Bayan da ta isa gaba cikin sa'a ne dai sai ta fadi ta suma. Nan da nan rakumin dawa ya zo ya dinga daddana mata cikinta har sai da ruwan da ta shaka ya gama ficewa tas daga cikinta da baka da hanci. Bayan farfadowar barewa ne fa ta harari rakumin dawa ta na mai cewa: Ashe daman kashe ni ka yi niyyar yi? Rakumin dawa ya ce me ya sa ni kuwa zan yi yunkurin kashe ki barewa? Barewa ta ce ai ce min ka yi fa ruwan iya kauri ya ke. Rakumin dawa ya ce e haka na ce mana amma ai cewa na yi iya kaurina ba kaurinki ba ko? Bayan da barewa ta kalli rakumin dawa ne fa daga sama har kasa ne ta dawo hayyacinta na gane cewa kaurin rakumin dawa fa ba sa'an na ta ba ne.
A nan fa barewa da rakumin dawa duk su ka bushe da wata bazawarar dariya su na cewa: "Hakika duk wanda ya daka ta rawar wani zai rasa turmin daka tasa;"
Comments
Post a Comment