BORI YA KAR BOKA
BORI YA KAR BOƘA
Wani mugun boka ne dai wami mugun bokanne dai. Ya kasance ya na baiwa azzalumai magunguna su na illata ko ma salwantar da rayuwan mutane da yawa a baya. Ya yi sanadiyyar haukacewa da bacewar mutane masu yawa a cikin wannan kazamin aikin nasa.
Idan mahasada su na son ganin bayan wanda su ke yi wa hassda to wajen wannan maketacin bokan su ke zuwa. Ya na kan sharafin sa na halakar da jama'a ne sai aka samu wata mata mai suna Afiruwa ta ba shi wani aiki na salwantar da kishiryata Hanne. Bayan boka yankarbi wannan aiki ya buga kasa ya sake bugawa har sau uku. A na hudun kuwa sai Afiruwa ta ga ya bata rai ya mulmulo wata irin ashariyar da bata taba jin irin ta ba ya kundumo. "Mu za'a yi wa haka?" Boka yabfada ya na wani irn wuci mai ban tsoro. Afiruwa ta ce me ke faruwa ne Baban Tsumbur? Ya ce mata wannan aikin ba karami ba ne amma ko mai zai faru sai mun yi shi. Wannan kishiyar ta ki a tsaye ta ke amma ba za mu taba bawa Tsumbur kunya ba.
Ya fada mata duk kayan da za ta tanada na turaruka da kuma nau'in kazar da ya ce a kawo za'a yanka ta baya a makabarta da talatainin dare. Duk abubuwan da Boka Baba Tumbur ya ce a tanada sai da Afiruwa ta nemo ta kawo masa duk da wahalar samun da wasu kayan kulumboton ke da shi. Bayan boka ya gama hada siddabarun sa tsaf sai ya dauko ya baiwa Afiruwa ya ce ga shi ta tabbatar ta binne su inda Hanne za ta tsallaka kuma ta tabbatar a lokacin ta na al'adar ta ne. Amma fa boka sai da ya fadawa Afiruwa duk abinda zai faru idan wanna aikin bai yi nasara ba. Ya fada mata cewa da shi da ita duk sai abinda aka shiryawa Hanne ya komo kan su. Saboda bakar zuciya irin ta Afiruwa haka ta amshi kayan nan ta na godiya.
A bangaren Hanne kuwa ta kasance baiwar A''ah mai yawan ibadun nafila da kuma kula da duk wajibai akan lokaci. Duk wata addu'ar falala ko ta neman tsari da ta ji a wajen malamai ko da a rediyo ne kuwa sai ta yi kokarin haddace ta da karantata a kullum. Mai gidan su duk ya sanya su a makarantar neman sanin addini, amma Hanne ce kadai ta ke zuwa ita Afiruwa ta ce duk munafunci wani sanya hijabi ana tafiya islamiyya gulma.
Bayan da Afiruwa ta dawo guda ta yi duk binne binnenta da barbade barbadenta ne, sai Hanne ta yi wani mummunan mafatki a daren da mai gidan su ya na dakin Afiruwa. A daidai lokacin da ta farka ne sai ta tashi ta sake alwala bayan wadda ta ke yi ta kwanciya barci. Sai da ta kwana ta na sallah ta na hutawa ta yi yan addu'o'i a tsakiya. Bata sallame ba sai daidai lokacin da aka fara kiran assalatu. Bayan ta gama ta yi sallar asuba ne ta kama lazumi har wayewar gari.
Hanne na kan dardumar ta bata gama wuridinnsafiya ba sai ihun Afiruwa kawai ta fara ji. Wayyo na kashe kai na! Wayyo na shiga uku! Ba shiri Hanne ta taso ta fito tsakar gida. A nan ne ta tarar da mai gidan su rike da Afiruwa tana ta samabatu tana fufusgewa ta na fadin wasu kalamai. Daga cikin abinda ake iya ganewa ta na cewa: Shi kenan yau za mu mutu ninda shi. Wa'lahi mutuwa za mu yi!" Da Hanne da mai gidan na su duk su ka bide baki su na kallon ikon Allah. A cikin wannan sambatu na ta ne duk ta gama zayyane abinda su ka shirya saboda su ga bayan Hanne. Amma Allah bai nufa ba. Bayan ta gama wannan sambatu da turje-turje da gaggatsa harshenta ne sai kuma aka ji ta yi wani irin ihu mai karfi ta daina motsi
Nan take Hanne ta kara gidea Allah da ya tsareta shattin mahasada masu kwana kulla tsiya.
Bayan kwana uku da afkuwar wannan abu ne makotan gidan Boka Baban Tsumbur su ka fara jin wani irin wari mai kidima dan adam ya na tasowa daga gidan Bokan. Bayan da aka tara matasa majiya karfi su ka balle kofar sai ga bokan kwance a daki har ya kumbura suntum wata irin mugunya na fitowa ta bakinsa da hancinsa kai har ta kunnensa. Bayan mutane duk sun ji abubuwan da su ka faru haka nan aka je a turbude boka a can bayan gari domin kwa malamai sai da su ka bada fatawar kada a kai shi makabartar musulmai domin bikanci kafirci ne. Haka aka hada gawar da matasa yan magaru su yi mata turbudewa irin ta jaki a can bayan gari.
Kurunkus!
Comments
Post a Comment