DODANNIYAR KUKA
DODANNIAYAR KUKA
A dajin Kalgo da ke Kasar Gobir akwai wata shu'umar bishiyar kuka da mutanen yankin su ka sanywa suna Dodanniyar Kuka. Wannan bishiya bishiya ce mai ban tsoro da kallonta. Tsofaffi sun shaidawa jikokin su cewa su ma kakaninsu sun fada musu cewa wannan bishiyar tafi shekara duba bakwai. Ko ina jikinta jijiyoyi ne daga sama har kasa. Sannan wasu lokutan akan ga wani ruwa kamar jini ya na kwaranyowa daga jikin jijiyoyin nan nata.
Dayawa mutane ba su san asalin abinda ya sanya ake ganin wannan jinin ba sai dai mazauna wajen su na da camfe-camfe iri-iri akan wannan dattijuwar bishiyar. Wasu sun ce mayu ne ke anfani da ita wajen shaye ko tsotse jikin duk wanda ya je kusa da ita. Wasu kuma su ka ce ai dodo ne a cikinta da ya ke fitowa tsakar dare domin dauke mutane ya shige da su cikinta ya cinye su. Wani bangaren kuma su ka ce ai muggan iskokai ne a cikinta kasancewar daman ai bishiyar kuka ce. Da dai sauran irin wadannan tatsuniyoyi da camfe-camfe da aka gada tun iyaye da kakanni.
Bayan an dauki dubban shekaru ana tsoron dodanniyar bishiya da kuma daukar da wasu ma su ka finga yi mata a matsayin abar bauta ne sai aka turo wani baturen gona daga birni zuwa Kasar Gobir. Bayan da ya sami wannna labari ne ya ce wa sarkin garin a bashi dama ya je ya yi bincike na kimiyya akan wannan bishiya. Da farko dai sarki ya yi kokarin hana shi don tsoron kada wani mugun abu ya same shi hukuma ta zo ta na tuhumar masa. Amma daga baya bayan ya ga wannan baturen gina ya dage sai ya bashi daman.
Baturen gona ya debi kayan aikinsa ya zuba a cikin wata jakar rataye ya nufi daji cikin rakiyar wasu amintattun fadawan sarki guda uku. Shi kan sa Baturen gona sai da ya ji tsigar jikinsa ta yi wani yarr yayinda ya kalli Dodanniyar Kuka daga nesa. Har ya yi niyyar ya koma amma sai ya tuna yanda ya dinga yi wa sarki kurari da ilimin kimiyya sai wata zuciyar ta ce masa: "kai tsaya kada ka baiwa maxa kunya mana." Haka nan dai Baturen Goma ya yi ta maza ya dakata. Bayan ya karbi jakar sa ta kayan aiki. Ya dan yi wasu aune aune sai ya gano cewa wannan bishiya tana daya daga cikin nau'in shuke-shuken nan ne masu cin nama. Eh cin nama mana. Domin su wadannan nau'in bishiyoyi bayan ruwa da iska da haske su na sarrafa sinadaren da su ke samu daga kwari da yan kananun dabbobin da su ke cafkewa a matsayin abinci misamman lokacin fari
Wannan binke ya zamo babban cigaba a gannin ilimin kimiyya kuma mutane da fama suna zuwa wannan daji na Kalgo domin yawan bude idanu da kuma nazarin kimiyya akan Dodanniyar Kuka
Comments
Post a Comment