FALALU FALKE A BIRNIN BADUN

FALALU FALKE A BIRNIN BADUN

Falalu shahararren falke da ya yi suna a ƙasar Hausa shekaru aru-aru kafin zuwan Anasara. Ya kasance mutumin Darazau ne shi. Ya kan je fatauci tun daga Darazau har sai ya dangana da Gwanja inda ya ke saro goro sannan kuma ya kai musu kayan mu na nan ƙasar zuwa can. Wannan ce sana'ar da shi ma ya gada a wajen mahaifinsa inda shi ma din ya gaje ta a wajen mahaifinsa.

Yana cikin wannan sana'a tasa da ya gada sai ya je Birnin Badun wata shekara inda ya tarar da ana wani bikin gargajiya wanda idan aka sami wamda ya yi nasara za'a aura masa ƴar sarkin garin. Saboda tsabar yarda da kan sa sai Falalu ya shiga cikin wannan gasar gaba gaɗi ba tare da ya san abokan gwabzawar sa ba ma. Ita wannan gasar dai ana haɗa kokawa ne tsakanin mutane biyu duk wanda kuma ya yi nasara shi ne zai gwabza da nagaba.

Bayan Falalu ya bayar da sunan sa ne sai ya hango wani gabjejen mutum ne abokin karawar ta sa. Falalu ya yi kamar ya janye takarar sa amma ya ji tsoron jin kunya da kuma kare martabar ƙabilar sa ta Hausa a idanun mutanen wancan garin. Haka nan ya tsaya ƴa fuskanci wannan Kutunkun ɗan damben cikin jarumta da nuna mazantaka. Da fari dai sai da ƙaton nan ya fara wasan kura da shi kafin daga bisani Allah ya bashi sa'a ya gano cewa wannan ƙaton baya son a dake shi akan agarar sa. Ai kuwa da Falalu ya gano hakan ya daga wani tsalle ya taka masa agara sai ya yi wata ƙara ya faɗi kasa wanwar ya na shure-shure.

Aka kirawo mutum nagaba nan ma ya yi nasara akan sa. Haka aka dinga yi Falalu ya na gamawa da su cikin ƙwarin gwuiwa. Daga ƙarshe aka bashi duk kyautukam da ake bawa wanda ya yi nasara da kuma amarya wato gimbiyar masarautar Birnin Badun.

Haka ya tawo da ita gida da ɗimbin dukiyar da ya samu sakakon wannan yawon fatauci nasa ga kuma amarya ga sauran kyautuka masu darajar gaske. Har yanzu zurriyar sa sana'arsu kenan kamar yanda kakannin su su ka ɗora su akai kuma su na samun cigaba da zamanantar da ita.

Ƙurunƙus!

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya