GATSORIYA MAI CIZON YARA
GATSORIYA MAI CIZON YARA
Ga ta nan ga ta nan ku!
Wani yaro dai dai wani yaro ne dai da ake ce masa Gatsoriya saboda ya da zako zakon hakoran gaba. Sunan sa na gaskiya dai Garbati. Tun ya na karamin yaro ya ke cizo mutane. Kai hatta Innarsa ma ya na wata shida tabyaye shi domin yada kwallon mangwaro domin ta wuta da kuda.
Garbati ko na ce mu ku Gatsoriya bai bar wannan dabi'ar ta sa ba har ya kai shekara hudu. Wata rana ana bikin dangi na yan maza zar har aure uku a gidan su na yawa. Sai wata Goggonsa ta lura da yanda Garbati Gatsoriya ya ke addabar yayan jama'a da cizo. Sai da ta kai duk iyayen yaran da su ka hango Gatsoriya sai su fara sungume yayansu suna goyewa don gudun kada su sha cizon Garbati Gatsoriya.
Bayan an dauki lokaci wannan Goggon na sa ta lura da yanda Garbati ya zama dodo abin tsoro ga yara da ma iyayen yaran. Sai kawai aka ga ta famko hannun Garbati ta ganyara masa cizo bayan da ga ya ciji wata yar afiruwar yarinya ta goye har sai da shatun hakoran nasa na gaba masu kama da garma su ka fito a dan mitsitsin hannun yarinyar nan. Nan take kuwa kallo yan koma sama. Kowa ya dawo ya na kallon Goggo Giwa ta na huci. Shi kuwa Garbati Gatsoriya sai faman rusa kuka ya ke yi tunda daman ance wanzami ba ya son jarfa.
Yayinda Goggo Giwa ta ga wasu matan suna wasu yan gunaguni sai ta daga murya ta ce: "Shari'ar cizo--cizo! Kuma Wal ciza bil cizi haka ma aka ce a karatun hadishi." Ai kuwa nan da nan kowa ya goyi bayanta aka cigaba da tattauna batun ana raha. Daga wannan lokaci ne fa duk sauran yayan jama'a su ka samu su ka sake a gidan bikin nan. Kowane yaro ya saki jikinsa ya na wasa da dan uwansa ba tare da tsoron farmaki daga Gatsoriya ba.
An ce tun daga wannan rana dai Garbati Gatsoriya bai kuma cizon kowa ba. Kai har ta kai ma baya barin wani yaron ya yi cizo a gabansa domin da zarar ya hangi wani yaron ya wawuro hannun wani zai gasa masa cizo sai janyo Larabcin nan na hadishin Goggo Giwa cikin tsamin baki irin na sa na yarinta ya ce:
"Goggo ta ce: Bil chijo bil chijo!"
Kurunkus!
Comments
Post a Comment