GILLARI GIRBAU SARKIN KARYA
GILLARI GIRBAU SARKIN KARYA
Liti wanda yanzu kowa ya fi sani da Girbau ya kasance mutum wanda ya shahara da ƙarya a garin Farin Duma. Ya soma wannnan mugun hali na sa ne tun ya na matashi. A halin yanzu kuwa ya haura sheka saba'in amma kullum abin sia gaba ma ya ke yi ba baya ba.
Ya na da iyalai har da jikoki da ƴaƴan jikoki amma har jikokin sa sun san lokutan da ya ke sakin baki ya girbota, to abin ka da sabo wai gawa da gatsine. Duk lokacin da ya ji jikokin nan nasa, cikin zolaya sun ce: "Allah ko Kaka?" To fa ya girba abar tasa kena wato dai ƙarya. Wasu lokutan ya kan sha jinin jikikln sa da zarar ya ji sun fadi waccan kalmar, amma sai ya ɓuge da borin kunya ya na cewa: "To ku na nufin na yi abar kenan ko?"Amma sau tari idan labarin ya yi masa daɗi to baya dakatawa sai ya kai ƙarshe.
Yana cikin wannan hali na sa ne har aka zo lokacin da za'a yi naɗin wasu sabbin muƙamai a masarautar su ta garin Farin Duma. A wannan lokaci ne sarkin garin ya sa aka naɗa masa sarautar Sarkin Ƙarya. Ya kasance kuma ya kan je fada wasu lokutan domin shirgawa sarki da jama'ar fada labarun ban dariya ma su cike da zulaƙe da shaci-faɗi. Wannan abin ya na baiwa sarki da makusantansa matuƙar nishaɗi da ɗebe kewa.
Lokacin da shekarun sa su kai kai wajen tamanin da biyar sai wani mashahurin malami kuma sharifi ya sa aka kirawo ma sa shi ya je har gidan sa ya yi masa wa'azi mai yawa kan illar ƙarya. A wannna lokacin sai da gemun Girbau ya jiƙe sharaf da hawaye sabida yanda wa'azin nan ya shige shi. Tun daga wannan ranar ce fa Girbau ya yanke shawarar ajiye wannan muƙamin nasa na sarkin ƙarya yayinda daga bisani ya koma ladanin masallacin unguwar su har zuwa lokacin da Allah ya karɓi rayuwarsa ya na ɗan shekara dari ba daya.
Comments
Post a Comment