GIZO YA ZAMA GIWA

GIZO YA ZAMA GIWA

Gata nan ga ta nan ku!
Gizo ne dai ya je rafi neman abinda zai kawo wa ƙoƙi ta dafa musu. Yana cikin shawaginsa a gaɓar rafi sai ya hangi wata kwalaba mai ɗauke da wani irn abu mai kauri kamar zuma a ciki. An dai rufe saman bakin kwalabar da wata irin fatar guza mai sheƙi sannan an rubuta cewa: "Kada ka buɗe kwalabar nan sai idan ka san cewa ta ka ce." Shi dai Gizo bai ma san abinda aka rubuta ba saboda tun yana ƙarami ya daina zuwa makaranta don haka bai iya karatu da ruɓutu ba dole sai dai ya kaiwa Ƙoƙi ta karanta masa.

A nan dai ya haƙura da nemo abimda da za su cinya tawo da sauri gida wajen Ƙoƙi. "Ƙoƙi Koƙi jo nan mun shamo aijiki" Haka Gizo ya dinga kiran Ƙoƙi cikin ƙaguwa da zumuɗi. Ƙoƙi na karɓar kwalaba nan ta duba sai ta ga abinda aka rubuta ɓaroɓar a jikin fatar nan da badukku ya ɗinke bakin kwalbar da ita. Nan take ta cewa Gizo ya yi sauri ya mayar da wannan kwalabar tun da dai ya san ba ta sa ba ce ba. Anan fa Gizo ya hau ƙoƙi da faɗa ya na cewa: "Saboda kin iya hasshada da baƙin tiki sai in samo aijikin sannan kijo ki te wai na mayai?" Ƙoƙi ta ja gefe ta na cewa: " To Allah ya baka haƙuri Maigida" ta shige ɗaki abinta.

Bayan Gizo ya yi fama kafin ya farke wannan fatar da aka rufe kwalabar a ƙarshe dai ya yi nasarar buɗe ta. Ya na buɗewa sai ya ga ruwan nan da ke ciki ya ƙara kauri a lokacin da iska ta taɓa shi. Abin ka da Gizo saikin kwaɗayi bai tsaya wata wata ba sai kawai ya ɗaga kwalabar nan sama bai dire ta ba sai da ya ɗaɗɗake wannan abinda ke ciki mai.kamar ruwan zuma. Bayan ya yi gyatsa ne kawai sai ya ji cikinsa ya ɗagowa ya na ƙara kumbura. Kafin ƙiftawa da bismilla cikin Gizo ya kumbura ya yu suntum.

Duk gaɓɓansa su ka dinga yin tsayi su na kauri. Ya dinga kiran Ƙoƙi cikin kuka ya na cewa: Ke Ƙoki ke Ƙoƙi jo ki ga yanda na ke ta komawa tun bayan da na shanye abin tikin kwalabai nan" Ƙoƙi na fitowa daga cikin ɗaki sa ta rafka salati mai haɗe da kururuwa. Nan take maƙota duk su ka shigo gidan su na tambayar lafiya? Lafiya? Kafin su rufe bakin su su ka ji wata irin muryar mai kama da gurnanin dodo na cewa: "Ku taimake ni ni ne Gizo mijin Ƙoƙi!" Nan da nan masu kawo gudunmawa duk su ka dinga kokawa wajen ficewa daga gidan saboda tsabar razanar da su ka yi. A nan ne ita ma Ƙoƙi ta bi su ta na cewa: "Allah ƙaddara saduwar mu, ni ma ba zan iya zama da kai ba a haka Maigida"

Maƙotan Gizo ba su tsaya ko ina ba sai ƙofar fada inda su ka kwashe duk abinda idanuwan su ka gane musu su ka faɗawa sarki. Sarki ya shirya tawagar mayaƙa, mahaya ɗawaki da ƴan baka na ƙasa ya ce aje a fitar masa da wannan halittar can bayan gari. Mayaƙan sarki na doso giɗan gizo sai su ka ga har ya rushe katangar gidan ya kuma rushe kan soro garin fitowa saboda ya zama gundumemiyar halitta kamar giwa.

Mayaƙan sarki na ƙoƙarin ƙaɗa shi zuwa hanyar wajen gari shi kuma ya na cewa ni ne fa Malam.Gizo mijin Ƙoƙi. Ni ma fa nan ce mahaifata. Ina ku ke son na koma to? Baraden sarki dai ko tsayawa ma su saurari sambatun Gizo ba su yi domin cika umarnin Sarki. Haka nan su ka raraka shi har bayan gari saboda gudun kada ya cigaba da ɓarnar ruguje mu su gidaje a ƙoƙarin sa na yawatawa a cikin garin. Bayan sarkin ƙofa ya janyo kofa ya rufe, Gizo ya zauna a bayan ganuwa ya yi kukan da ya ishe shi sannan ya tashi ya nausa cikin jeji inda a can ne ya ƙare rayuwar sa cikin namun dawa ba gida ba kuma Ƙoƙi matar sa ta lalle.

A daidai nan sai Iya mai tatsuniya ta ce: "Yara yara!" yara su ka amsa: Iye! Iye! "Kada wanda a cikin ku ya ga kwalabar magani ya buɗe ya kama sha saboda duk wanda ya sha maganin da ba Innar sa ce ta ba shi da kanta ba to zai zama gundumeme kamar Gizo kuma ƙarshe dai duk kun ga abinda ya faru ga Gizo ko? Duk yaran su ka haɗa baki su ka ce: "e Iya!"

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya