JUMMAI KUNYA
JUMMAI KUNYA Ga ta nan ga ta nan ku! Wani yammaci wasu ƴan mata har su bakwai su ka je yin itace gefen gari. Waɗannan ƴan mata sune: Asabe, da Ladi, da Atine, da Talatu, da Larai, da Lami da kuma Jummai. Dukkannin su gidajen su maƙoftan juna ne. Bayan sun yi nisa a dawa ne har sun fara yin itace wasu ma har sun fara ɗaure na su, ai kuwa sai wani baƙin hadari ya gangamo daga gabas mai haɗe da iska. Tunda su ka ji sanyin ruwa a cikin hadarin nan su ka sha jinin jikin su cewa wannnan hadarin idan ya tsinke da ruwa sai wani ikon Ubangijin ne kawai zai tsayar da shi. Ai kuwa kafin su gama shawara ruwa mai ƙarfi ya kece. Nan fa su ka nemi wata ƙatuwar bishiyar kuka mai kogo su ka shige ciki. Bayan sun shiga kogon bishiyar kuka nan sun fake ne, kawai sai su ka dinga jin ƙasa ta na motsi. Ashe dodo ne ya zo daf da wannan bishiya ya zauna ya jingina bayansa a daidai ƙofar fita daga wannan kogon bishiyar. Nan fa wannan kogon ya ƙara yin duhu dinɗum ta inda babu mai iya ganin ko da tafin hannunta...
Comments
Post a Comment