KALELE BARBAƊIN TUSA

KALELE BARBAƊEN TUSA

Ga ta nan ga ta nan ku!

Akwai wani yaro mai wata mummunan al'ada ta sakin tusa a cikin jama'a ba kan gado mai suna Kalele. Ya kasance ya na aikata wannan abu tun ya na ƙarami. Wasu lokutan idan aka zauna da shi  har sai ya kumburawa duk waɗanda ke wannan wajen cikin da warin tusar nan da ya ke gunsurawa.

A lokacin da yara ƴan uwan sa su ka fuskanci ya na illata su, sai duk aka daina zama  a inda ya ke ko kuma da zarar shi ya zo cikin yara ya zauna, duk sai kowa ya watse. Wannan abin ya na damunsa amma ya rasa mafita.

Ana haka har ya zama saurayi. Duk sauran tsaraikunsa sun samu ƴan mata har magana ta kai ga manya ana shirye shiryen aure, amma shi duk wajen yarinyar da ya je sau ɗaya ba ta yarda da ƙara fitowa ta biyu saboda yanda ya ke sakin abar ta sa ba kan gado kafin su gama taɗi.

Ana cikin wannan hali ne sai aka yi wani baƙon wamzami mai bayar da mugunguna. Ya cire kunyarsa ya je ya yi wa wanzami bayani dalla-dalla. Sai wanzam ya ce da shi ga wasu magunguna na sha da na hayaƙi, sannan kuma ya ba shi shawarar kan cewa ya dinga yawan shan ruwa sannan ya tabbatar kullum ya na shiga magewayi a ƙalla sau ɗaya a rana kuma ya dinga tabbatarwa ya gama biyan buƙatarsa tsaf  kafin ya gaggauta yin tsarki ya fito. Haka nan kuma wanzam  ya ƙara masa da cewa kada ya kuskura ya ƙara sakinta sasakai a cikin jama'a. "Da zarar ka ji alamun fitar ta, to ka yi hanzari ka bar wajen ka yi nesa da jam'a sannan ka yi. Idan kuma ka san cewa ka ci wani abu da kasan ya kan ɓata maka ciki, to sam ka da ka shiga cikin tarukan al'umma a wannan ranar." Wanzam ya ƙarasa masa bayinin cikin tausawa da kulawa.

Bayan Kalele ya fara anfani da waɗannan shawarwari na wanzam ne aka nemi wannan lalura ta sa sama ko ƙasa aka rasa, domin kuwa yanzu kowa ya na iya sakin jiki da shi ayi mu'ala mai daɗi kuma cikin dafin rai ba tare da ƴa gunsuro abar nan tasa da aka san shi da ita a baya ba.

Sai dai kuma tarihi ya adana mana wannan sunan nasa ga shi nan har yanzu yaran da ma ba su san wannan labarin ba suna jin sunan na sa ƙarshen waƙar Najajjeni Gidan Gwauro........

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya