KARE MAI GEMU

KARE MAI GEMU

Gata nan gata nan ku!
A yankin Bakin Kasuwar Kurmi da ke gefen Kogin Jakara a Kasar Kano an yi wani kare mai ban al'ajabi da kuma ban tsoro. Shi dai wannan karen duk dan shekara tamanin zuwa sama ya san shi. Imma dai shi ma ya taba ganin sa ko kuma ya ga wanda ya taba kacibis da shi a cikin matsa masu yawon dare 

Kare ne mai ban mamaki wanda ya ke yawo a kewayen kasuwar domin hana bata gari aikata mummunan aikin fasa shaguna da sauran laifukan bata gari  Wadanda su ka ga wannan karen sun tabbatar da cewa ya na yin magana kuma wuyansa daure ya ke da wata irin murtikekiyar sarka ta bakin karfe har ta na jan kasa. Duk sanda ya fito makotan yankin kan ji karar wannan sarkar da ke wuyansa tana jan kasa kachacharr-kachacharr-kachacharr! Dattawa da matasan wancan lokacin sun kasance idan sun gama da shi su na yi masa sannu ko su gaishe shi kuma shi ma ya na amsawa cikin mutuntawa. Babu wanda ya ke nufar sa da wani mummunan abu shi ma haka nan ya ke zaune zaman amana da jama'ar yankin 

Bayan da shekaru su ka lula ne, sai yaran zamani da su ka sami labarin wannan kare ya na fitowa da dare su ka dinga zama har sai lokacin fitowar sa ya yi domin kawai su dinga tsokanarsa su na jifansa. Duk sanda ya fito sai su dinga tsokana su na cewa: 'Kolo ne! Kolo ne!" Da farko farko dai ya kan ba su amsa da cewa: "Gyatumin ku ne kolo!" Amma da ke ya hadu da yaran zamani kamar ma kara zuga su ya ke idan ya mayar musu da martanin. Sai kawai ya ga sun cigaba da jifa da eho. Wadannan dalilai su ka sanya dole ya hakura ya daina fitowa 

Bayan wannan kare dan amana ya daina fitowa ne sai kuma sace sace a gidaje da fasa shagunan kasuwa da barna iri-iri su ka dinga faruwa a yanki da kewayen Bakin wannan tsohuwar kasuwa mai tarihi ta Kurmi. Manyan dattawa su ka tambaya shin ana ganin Kare mai Gemu kuwa yanzu? Duk jama'ar da ke wajen su ka tabbatar musu da cewa ai matasa marasa ji ne su ka dinga jifan sa da tsokana yanzu dai sama da watanni shida kenan ba'a kara jin duriyarsa ba. Wadannan dattawa su kai bakin ciki sosai kuma su ka nuna bacin ran su game da wannan abu da yaran su ka aikata. 

Wani dattijo da ya kasance ya girmi kowa a wannan kewayen ya tabbatarwa da jama'ar da su ka taru cikin takaici da alhini cewa: "Wannan karen kakana ma yace haka su ka taso su ka tarar da shi. Ba ya cutar da kowa sai ma kokarin  kare jama'a da dukiyoyin su. Yanzu ga shi wasu tsirarun tsageru sun korar ma na shi."
Haka nan dai kowa ya dinga Allah wadai da wadannan matasa ma su kunnen kashi.

Kurunkus.

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya