KYAN ƊAN MACIJI
KYAN ƊAN MACIJI
Akwai wata kyakkyawar yarinya a garin Ƴan Kwaɗi mai matuƙar jiji da kai da raina mutane sabida ganin kyawun da Allah ya yi ma ta. Tun da aka haifeta aka ga irin zubin da Allah ya yi ma ta mahaifiyar ta ta sanya mata suna Tafisu. Har wata waƙa ta ke yi mata ta na cewa
"Kin fi su kin fi sauran mata
Kyawu gare ki ya fi kwatanta
Mai aurarki sai fa wanda ya huta
Kai koma da baya hannu kanta"
Tun Tafisu ba ta san me ake nufi da wannan waƙar mai haɗe da kirari ba take jin matuƙar daɗi da alfahari a duk lokacin da mahaifiƴarta ta ke rera mata wannan waƙar. Duk ƙawayenta ta mayar da su ne kamar wasu barorint ko ƴan kore, kai, hatta waɗanda ma su ka girme mata a shekaru ta raina su domin kuwa har ta na iya aikensu duk sanda ta ga dama kuma dole su je saboda kwatjinin da Allah ya bata da kwaɗayin cigaba da zama a cikin muƙarrabanta.
Idan ta raina yarinya kuwa ta na zuwa waje sai ta ce ita wari ta ke ji kuma ta dinga toshe hancinta. Haka nan duk sauran ƴan kanzaginta su ma za su dinga tattoshe hanci don kawai gudun kada ta yi fushi da su ta kuma daina ƙawance da su.
Ta na wannan hali na ta ne dai har ta zama cikakkiyar budurwa. Anan ne fa ta ƙara tsiro da sabbin abubuwa na taƙama da ƙasaita.
Wata rana da yammaci bayan duk ƴan matan garin su sun taru a dandali, sai ta fito tsakiyar ƴan gaɗa ta rera wata waƙa inda ta ke cewa:
"Ni Tafisu ba ni auren kowa
Sai ko wanda ba tabo a jikinsa
Ya yi luwai luwai kamar wata tsada
Ni Tafisu na fi kowa tsada"
Tun daga wannan yamnaci ne fa ta kori duk ƴan samarinnta da su ka rage wai ita lallai sai saurayi marar tabo ko ɗaya za ta aura. Bayan an ɗauki lokaci kuma ta rasa samun saurayi marar tabo kamar yanda ta buƙata, sai ta sake zuwa da wata sabuwar gasar cewa wai duk wanda zai aureta sai iya jefa takwankwani guda bakwai a jere cikin wata ƴar ƙaramar hudar da ta sanya aka yi mata a tsakiyar murfin wani ɗan ƙaramin akushi. Duk samarin garin sun yi sun yi har sun gaji amma duk sun kasa cinye wannan gasar.
Daga cikin masu ƙaunar Tafisu har da wani baran gidan su mai yi musu hidima mai suna Barau. Amma saboda ganin yanda Tafisu ta ke wulaƙanta ƴaƴan manyan attajirai da sarakuna ma sai Barau bai taɓa gwada furta mata cewa ya na sonta ba ma don tsira da mutuncinsa. Sai dai wasu lokutan ya na nuna mata ta hanyar sakin murmushi marar dalili da kuma jin zafi a ransa idan ya ga tana cikin wata damuwa. A lokacin da ya ji cewa ta sanya wannan gasar kuwa har kwana ya ke yi ya na gwajin jefan murfin akushin nan a kwanankin hasken wata. Tun ya na gaza samun shigar ko da tsakuwa guda ɗaya, har sai da ta kai ya na iya jefa duk bakwai ɗin a lokaci.guda ba tare da ya kaucewa ko guda ɗaya ba.
Bayan Barau ya gama gwajinsa ne ya bugi ƙirji shi ma ranar kasuwa bayan an fara gasar nan domin nuna tasa bajintar. A nan fa kowa ya dinga dariya, kar ma a ce mu ku Tafisu ganin yanda ta raina ƴaƴan manya ma ballantana wannan da ya ke kamar bawan gidan su. Har ta yi nufin a hana shi sjiga gasar sai kuma ta ce a bar shi ya gwada cikin izgili da ɗagawa.
A lokacin da ya jefa tsakuwa ta huɗu a jere kuma duk su ka shiga cikin akushin nan a daidai, sai fa waje gaba ɗaya ya ruɗe da sowa da tafi. Yayinda ya zo jega cikon tsakuwa ta bakwai kuwa sai aka dinga bada waƙa ana amshi ana ana cewa:
"Kai ne mijinta kai ne mijinta
Kai ne mijinta duk mun yarda
In ka cike bakwan ta yarda
Ko ba ta yarda ba mun yarda
Walla Barau fa ɗan sa'a ne
Kun ji Barau masoyin Tsaɗa"
Lokacin da zai jefa cikon ta bakwan dai Tafisu har runtse idanuwanta ta yi ta na ta fatan Allah ka da ya ba shi nasarar cinyewa. Ba ta buɗe idsnunta ba dai sai da ta ji ƙawayenta su na cewa: "Yawwa ya faɗi dai a karshe." A hankali ta buɗe idanunta tare da yin wata ajiyar zuciya mai cike da godiya ga Ubangiji.
A na nan kwatsam a wata ranar kasuwa, sai ga wani kykkyawan saurayi wanda babu wanda ya taɓa ganinsa a garin. Bayan an gama cin kasuwa har duk ƴan matan garin sun hallara a dandali ana shirin fara gaɗa ne, sai shi ma ya je wajen domin kashe kwarkwatar idonsa. Da zuwansa hankalin duk ƴan matan nan ciki har da Tafisu ya dawo kansa ganin irin zubin kyawun tsari da Allah ya ƴi masa. Tafisu har saida ta dinga faɗi a ranta ta na cewa: "Wannan ko duk jikinsa tabbai ne zan aure shi a haka."
Bisa mamakin duk waɗanda ke wajen sai aka ji ya ce shi baƙon Tafisu ne kuma zuwa ya yi domin ya gwada sa'arsa a gasar da ta sanya ta nenan saurayi marar tabo ko kuma wanda zai jefa tsakwankwani bakwai a ciikin akushi a jere. Kyakkyawan saurayi ya ce duk da dai ya shi ya cika sharaɗi na farko na rashin tabon amma dole ne sai an ba shi damar gwada sa'ar sa ta yin jifan nan. Aka sanya wata ƴar tshuwa ta shiga da shi ɗaki ta duba shi sarai babu tabo ko guda a jikinsa daga kan sa har ƴan yatsunsa na ƙafa.
A ka kawo masa wannan akushin mai murfi nan take ya jefa duk tsakwankwanin nan guda bakwai a jere ba tare da ya kauce ko ɗaya ba. Nan fa aka ga murna a kan fuskar Tafisu bakinta har kunne.
A ka gabatar da kyamkkyawan saurayi ga iyayen Tafisu kuma aka tambayes hi sunan sa ya ce shi sunansa Dauda.
A wannan wajen nan take aka sanya ranar biki cewa mako mai zuwa ranar kasuwa za'a ɗaura auren su. Bayan an sha biki sai aka haɗa Tafisu da wannan hidimin gidan na su mai ƙaunarta wato Barau su ka rankaya da duk kayanta da kuma gararta zuwa garin su kyakkyawan saurayi Dauda.
Su na tsaka da tafiya sai Dauda ya nufi dokar jeji. Su ka tamɓaye shi sai ya ce ai shi nan ne hanyar garin nasu. Bayan an ɗan yi tafiya mai nisa, sai Dauda ya ce zai ɗan kama ruwa a bayan kargo. Bayan wani ɗan ƙaramin lokaci kawai sai ga Dauda ya fito amma duk rabin jikinsa ya koma na maciji sauran iya gangar jikinsa da kansa har da ɗan rawaninsa ne kawai ba su ƙarasa komawa na maciji ba. A nan ne fa da Tafisu da hadiminta duk su ka rkice aaboda tsoro.
Tafisu cikin kuka ta fara rera wata waƙa shi kuma Dauda ya na mayar mata ta amshi kamar haka:
"Dauda ina shakwararka?
Shi kuma Dauda ya na cewa:
Na barota cikin gona
Dauda ina taguwarka?
Na baro shi cikin gona
Dauda ina wandonka?
Na baro shi cikin gona
Dauda ina takonka?
Na baro shi cikin gona"
Kafin Tafisuu ta ƙarasa wannan waƙar hadiminta ya ranta a na kare ya koma cikin gari a gigiice ya na cewa: "Dauda ba mutum ba ne maviji ne!" Mutanen gari har iyayenta duk su ka ce ba za su iya zuwa domin ceto ta daga hannun shu'umin macijin nan ba. Barau ya yi kuka kamar ransa zai fita.
Bayan tafiyarsa ne Dauda ya ƙarasa zama maciji cikakke mai ban tsoro inda ya sanar da Tafisu cewa shi ɗan sarkin macizan garin su ne. Kuma ya san duk irn wulakancin da ta dinga yi wa jama'a a baya saboda kawai ganin kyawunta.
"To yanzu anan za ki zauna da mu na har abada cikin jeji a matsayin baiwa a garken macizai" Dauda ya faɗa ya na ƙarasawa da wata irin dariyar maƙetata.
Ashe ashe Barau ba guduwa ya yi ba zuwa ya yi ya sanar da mutan gari. Bayan ya ga cewa babu mai niyyar taima masa sai ya dawo gefen dajin ya samo ganyen magarya da ganyen aduwa da tazargade da tafarnuwa ya haɗa da ruwan Rijiya Biyu da ya ɗebo tun daga cikin gari, ya tofa wasu ayoyin tsari sannan ya ahiga dajin cikin sauri. Ya na zuwa ya laɓe a ƙan wata bishiya inda maciji Dauda ba zai gan shi ba . Sai da ya bari macijin ya zo daida ƙasan bishiyar sai ya watso masa ruwan tofin nan. Nan da nan wani baƙin hayaƙi da tururi su ka dinga tashi daga jikin maciji kuma naman macijin nan ya dinga zagwanyewa har dai a ƙarshe ya faɗi a ƙasa rigija ya mutu.
A nan ne fa Tafisu cikin hawaye ta godewa Barau kuma gaba ɗaya su ka dawo cikin gari. Tafisu ta ce ita yanzu duk ta daina wannan halin na ta kuma lallai ita Barau ma za ta aura saboda ta nuna masa halacci domin ceto ta daga ƙangin bauta a garken macizai.
Aka ɗaura musu auren bayan anyi kwana bakwai ana shan shagulgulan biki wanda aka daɗe a garin Ƴan Kwaɗi ba'a ga irin sa ba
Ƙurunƙus!
Comments
Post a Comment