LANTARKIN MUTANEN DAURI

LANTARKIN MUTANEN DAURI

A wani gari can wajen ƙasar Misra an yi wani masanin kufai da tarihi mai suna Ramzi Alhamdani. Wannan masani ya shahara wajen bincike kan dalar gyaɗar Misrawa da yanda su ke adana gawawwaki da sauran tatsuniyoyi da nazari kan Fir'aunoni da bayanai akan daulolin su.

Wata rana ya na tsaƙ da bincike sai ya tono wani abu mai kama da fitila. Cikin ikon Allah daɗewar da wannan abu ya yi a ƙarƙashin ƙasa bai sanya ya yi ko ƙwarzane ba. Hatta kwalbar da ke kewaye da abin ko tsagewa ma ba ta yi ba duk da irin nauyin ɓaraguzan da aka haƙe daga kanta kafin a riske ta. Kowa ya cika da mamaki akan menene wannan abin kuma ya ya su ke anfanin da shi a wancan lokacin?

Bayan ya je gida ya huta ya yi wanka sai ya ɗauki wannan abu ya shiga ɗakin bincike. Ya dinga ƙoƙarin buɗe shi har dai dare ya tsala amma ya rasa ganin makamar inda zai fara dagawa domin buɗe cikinsa don faɗaɗa yin nazari. Haka dai ya haƙura ya je ya kwanta cike da al'ajaba.

Ya na tsaƙa da barci ne sai ya yi wani mafarki ga shi a ɗakin binciken kimiyya ya ɗauko wanann abu ya sanya wata wuƙa mai tsini a.ƙasan sa ya danna wani maɓalli ciki kawai sai abu ya buɗe. Firgigit ya farka ya kuna tashi ya nufi ɗakin binciken. Ya na zuwa sai ya ɗaga ƙasan abin sai ga wannan maɓallin kuwa ya dannan kamar yanda ya ganin a mafarkinsa. Maimakon ya buɗe kawai sai ga wani irin haske mai tsanani ya cika ɗakin binciken. Kai ka ce da babu fitilu a cikin wajen. Nan fa masani Alhamdani ya ƙara cika da mamakin wannan abu.

Ya kuma danna wannan maɓallin sai hasken ya ɗauke sai kuma yaga wani rami a kusa da wannan maɓallin. Ya na zura wani ƙarfe mai tsini a rami sai ƙasan ya buɗe. Buɗewar wannan abu ke da wuya sai ga komatsan da ke ciki sun tarwatse a ƙasa kai ka ce daman wata ƴar tsirkiyar tsakiya ce ke riƙe da su kuma ta tsinke. Komai ya baje a ƙasa ba tare da ya ga gano yanda haɗin abin ya ke ba kafin ya tarwatse.

Komatsen da ya iya ganowa a cikin wannan abu dai akwai maganaɗisu guda biyu masu girma ɗaya, sai wani ɗan ƙarfe da aka lanyace shi da wayar tagulla, sai wani irin dutse mai kama da ƙanƙara sai kuma wata firfiluwa mai jujjuyawa wadda aka maƙala wannan ƙarfen mai lanyace da wayar tagulla a jikinta.

Nan dai Dr Hamdani ya kwana ya na ta koƙarin mayar da wanann abu kamar yanda ya ke amma abin ya ci tura.  Bai aune ba sai jin kiran sallah ya yi duk maslalatai sun fara. Ya je ya yi sallah ya ƙara dawowa kan bincike. Anan ne ma ya ya gano cewa wannan firfiluwar ce ke juya wayar nan tsakanin maganaɗin su mutanen da wanda idan ya kama ƙarfe sai an yi da gaske ya ke sakinsa saboda ƙarfinsa. 

Ya yi ƙoƙarin mayar da shi yanda ya ke amma hakan bai iya yi wu ba sai dai ya samo wani sabon ilmi cewa idan da za'a samo irin wannan maganaɗisun mai matuƙar ƙarfi to za'a ɗinga samar da lantarki ne ta hanyar mutanen da cikim sauƙi ba tare da anfani da manyan injina ba da ake sanyawa a madatsar ruwa ba masu ƙara da saurin lalacewa ko kuma masu anfani da gas da ke gurɓata muhulli.

A yanzu haka dai ana iya samun injin wutar lantarki da za ka sanya shi a aljihun ka saboda ƙanƙantar sa sakamakon wannan naura mai ban al'ajabi da aka gano a Misra.

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya