MAGANA MAI.DAFI
MAGANA MAI DAFI
"Kullum ku kasance ma su kyakkywan lafazi yayinda kuke magana domin wannan ma sadaƙa ce inji Manzo ASW" Wannan shi ne abinda Ilu ya tarar liman ya na faɗa akan minbari yayinda ya iso masallacin Juma'a. Bayan ya sami waje ya zauna ne sai ya yi tagumi kuma ya tsunduma cikin tekun tunani.
"Ilu! Ilu! Ilu! Ka tashi za'a tayar da sallah fa!" Cewar mutanen da ke kusa da shi a sahun sallar Juma'a. Ba shiri Ilu ya tashi ya je ya sake ɗaura al'wala ya zo ya riski sallah. Bayan an idar da sallar nan fa aka dinga tambayar Ilu dalilin da ya sa ya fita hayyacin sa lokacin da ake yin huɗuba har sai da kamar hankalimsa ma ya gushe.
Anan ya kada baki ya ce musu shi ya kasnace dan garin Tsaunin Ƙunci ne kafin ya tawo birni karatu da kuma nema. Bayan ya kammala karatu ne ya fara sana'oi har ya zama ya mallaki gida a birni.
"Na kasance mai yawan faɗawa mutane baƙaƙen maganganu duk lokacin da su ke tattauanwa da ni. Sanadiyyar hakan ne na rasa yawncin abokan da mu ka taso tare da su a ƙauye. Wasu ma sai da mu ka yi faɗa sannan mu ka rabu, wasu kuma da su ka ga take take na na kwakkwaɓa magana yanda na gadama su ka fita daga cikim al'amurana." Ilu ya cigaba da bada labari cikin alhini.
"Na zamo tamkar mujiya a cikin tsuntsaye kowa sai gudu na ya ke yi." Inji Ilu. "
Ban taɓa tunanin cewa rashin iya furta kalamai masu daɗi kan iya janyo wannan taɓarɓarewar alaƙar ba tsakanina da makusanta da maƙota da kuma abokai na ba. Sai yanzu da na ji huɗubar liman ta ratsa ni shi ne duk na fita daga hayyaci na." Ilu ya cigaba da ba su labarinsa har ya fara kwalla a daidai wannan lokacin.
Ya ƙara da cewa: "Akwai babban amini na ɗan uwa kuma maƙocin da tare ma aka yi ma na shayi amma sai dai mu ka yi baram-baram da shi kafin na baro kauye." Jama'ar da su ka taru duk su ka jajantawa Ilu kuma wasu su ka ba shi shawarar cewa tunda dai yanzu ya gane gaskiya, kuma ya na son ya gyara abubuwan da ya ɓata to dole sai ya fari daga can Tsaunin Ƙunci wato ƙauyen su.
Ilu ya koma gida domin sasantawa da ƴan uwa da abokansa tun na ƙuruciya. Kowa ya gani sai ya kira sunan sa cikin fara'a ya rungume ahi cikin nuna ƴan uwnataka da kulawa. Kowa sai buɗe baki ya ke ya na mai mamakin wannan gagarumin sauyi da ya samu Ilu rana tsaka. Bayan ya kwana biyu a garin sai ya sa aka shriya walima ga duk jama'ar sa da suka ɓata kafin ya je bitni. Ya nemi afuwar kowa da kowa kuma kowa ya yafe masa cikin murmushin da sakin fuska.
Tun daga wannan lokaci dai Ilu bai kuma faɗar magana ba haka sasakai sai ya tauna ta a bakinsa kafin ya furta. Haka rayuwarsa ta inganta cinikin sa a kasuwa ya ƙaru sakamakon iya zama da magana da jama'a sai da aka dawo kiran sa da sunan 'Ilu kowa na ka.' Shi kuma sai ya ce: "Banda munafuki da ɓarawo!" Sai kowa ya bushe da dariya.
Comments
Post a Comment