MAI ƘIRINIYA

MAI ƘIRINIƳA

Shawai yaro ne mai rawar kai da ƙiriniya wanda ko  yanzu mutum ya fara ganinsa sai ya fahimci hakan daga gare shi. Shi ko irin baƙuntar nan da yara su ke yi idan sun je baƙon waje ba ya yi. Ya na zuwa wajen duk sai kowa ya san shi kuma sai ya gallabi kowa da raahin ji. 

A lokacin da ya ke rarrafe ya taɓa janyo risho da girkin kan gaba ɗaya a jikinsa. Ya samu, inda wuta ta kama rigar sa ga kuma ƙunan da ya samu daga abincin da ke kan tukunyar. Ya samu munanan raunukan kuna a wancan lokacin amma abin ka da yaro ya na warkewa ya ɗora daga inda ya tsaya. A haka mahaifiyar sa ta taso cikin kaffa kaffa da shi don gudun ƙada ya illata kansa ko kuma wani ta hanyar wannan karambani da ƙiriniyar tasa.

Bayan ya kai shekara shida ne wata rana yana ciwon kunne sai mahaifiyarsa ta kai shi asibiti. Bayan an duba shi sai likitan ya lura duk da cewa ya na fama da ciwon kunnen amma wannan bai hana shi taɓe taɓe da karanbani ba a ofis ɗin sa. Sai ya tanbayi mahaifiyar cewa : "Shin tun yaushe ya fara hakan?" Sai ta ce masa: "Ai ina ga fa tun yana ciki ma ya fara. Domin ita bata taɓa samun cikkn yaro mai yawan motsi da zuruftu kamarsa ba." Likitan ya ɗanyi murmushi ya ce to wannan dai ba wani abin damuwa ba ne. Adinga dai ba shi kulawa ta musamman sannan a dinga kawo shi ya na ganin likita.

Likita ya ce: "A wajen likitoci ƙiriniya dai wata wata cuta ce da ke sanya yara da ma wasu daga cikin manyan kasa mayar da hankali kan abu guda da kuma rage sakar kuzarinsu ko ina barkatai. Akwai magunguna da shawarwari da za'a cigaba da baki bayan wasu lokuta duk zai daina, musamman idan an bi dokakin da sharaɗan abubuwan ma da zai dinga ci ko sha.zuwa wani ɗan lokaci.

Haka nan kuwa mahaifiyar Shawai ta dinga kawo shi ana bata shawarwari da wasu ƴan magunguna. Bayan wasu ƴan watanni duk sai abin ya fara janyewa a hankali. 

Kafinnan likitan ya faɗa mata cewa: "Ni ma na samu yarona  na cikins  na mai matsananciyar ƙiriniya. Har wata rana ma ya shiga cikin injin wanki da kyar aka zaro shi. Wata rana kuma ya shige ciken friza mai rijiya wai duk kawai don neman wajen ɓuya a lokacin da su na yin wasan ƴar burumburum da sauran ƴan uwansa. Allah ya sa dai anyi saurin ganinsa a lokacin da tuni ya zama kifi sadin". Likita ya ƙarasa faɗa cikin wata murya mai cike da raha da kuma kwantar da hankalin mahaifiyar Shawai.

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya