MAI KUKAN WANKA

MAI KUKAN WANKA

Gata nan ga ta nan ku!
A zamanin Sarkin garin Tugoru wanda ake kira Tankwa III ne aka haifi wani yaro mai suna Inuwa Na Najatau. Ana kiransa Na Jatau ne kasancewar sunan mahaifinsa Jatau kuma shi ne dan sa na fari. Tun ya na dan jariri baya kaunar wanka. Da an dauka kuriciya ce irin ta wasu yaran. Amma abin ya dinga gawurta har zuwa lokacin da ya cika shekara takwas bai daina kukan wanka ba.

A duk lokacin da aka ce ya yi wankan da kan sa kuma nan ma sai ya shiga bayi ya shekar da ruwan ya ce wai ya gama. An yi masa wakoki da ature iri-iri na mai kukan wanka amma ina abu sai gaba ya ke yi. Na Jatau a lokacin da aka haife shi jajur ya ke kamar tsada, amma zuwa lokacin da ya kai shekara takwas ya yi wani jurwaye da waskane da kirci kamar wanda aka tono daga rami.

Saboda tsabar rashin son wankan Na Jatau har sai da ya zama ya fara wari duk inda ya shiga ana kau da kai ga masu jin kunyar sa kenan. Amma wadanda su ke babu wata kara tsakanin su kai tsaye su ke toshe hancin su a gabansa.

Bayan ya zama saurayi ne dan kimanin shekaru goma sha biyar abokansa su ka shirya masa lalata. Sai da su ka bari watan Azumi ya kai kwana goma Na Lako ya cire tuga har ya zaga gari da yamma. Dare na yi sai su ma su ka samo tandu da talle su ka tufka wata murtikeniyar igiya inda su ka je gidan su Na Jatau aka sa aka yi sallama da shi. Gitowarsa ke da wuya kawai matasan nan su ka zarga masa igiyar nan a wuya su ka bade fuskar sa da bakin tukunyar da aka dama shi cikin man kafanya hade da toka. Su ka jawo da karfi zuwa waje suna kida su na yi masa wata waka mai ban takaci ga wanda ake rerawa ita:

Me kukan wanka,
Na Jatau
Yai girman banza,
Na Jatau
Ba ya son wanka
Na Jatau
Ya yi bakikkirin
Na Jatau
Sai faman wari
Na Jatau
Me kukan wanka
Na Jatau
Me kukan wanka
Na Jatau

Haka nan matasan nan su ka zagaya duk cikin garin Tuguro da abokin su Na Jatau. Ana kida ana waka shi kuma ya na ta sheka gursheken kuka ya na sussunkuyar da kai. Hakika idan ran Na Jatau ya yi dubu rannan ya baci. Ya shiga damuwa da kunci fiye da inda kowa ya ke iya tsammani.
Wannan abinda yan uwansa matasan abokan sa su ka yi masa sai ya zame masa gata, domin tun daga wannan ranar bai kara zama da kazanta ba. Kullum sai ya yi wanka akalla sau uku a rana. Kima ya na iya siyan turare komai tsadar sa. Wasu lokutan ma a wajensa tsaraikunsa ke ganin salon sabbin tufafin sawa, turare da sauran kayan ado da kwa'loya na kwalisa.

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya