MAIRAMA ƘANWAR MAZA
MAIRAMA ƘANWAR MAZA
Mairama yarunya ce wadda ke bin yan maza har bakwai a ɗakin su. Saboda haka da yawan mutane ke ce mata Dela. Mairamaa ta taso cikin maza. Tare su ke yin komai daga kan wasa har zuwa cin abinci da hira duk da ƴan uwanta maza ta ke yi kasancewa babu mata tsaraikunta a gidan da su ke wanda ya kasance gidan yawa ne.
Bayan da Mairama ta kai shekaru shida ne sai mahaifiyar su ta lura da yanayin irin halayen ƴar tata. Ta kan yi ƴar dungure da alkafura kamar dai yanda ta ga yayyanta maza su na yi. Ta fi shaƙuwa da Ali wanda shi ne sakonta. Duk abinda ya yi na ƙiriniyar yan maza to tabbas kuwa sai ta gwada yi. Mairama ta iya keke ta iya dambe da kokawa da sauran wasannin maza dai kamar su langa da makamantansu. Kai hatta maganar Mairama ta rikiɗe ta zama gwangwaram kamar ta maza.
Sau tari ba ta sha'awar ɗaura zani ko siket ma. Wannan ya sa yawancin kayanta ake ɗinka mata da wando ba zani ko siket ba domin kuwa ko an ɗinka zanin ma bata iya ɗaurawa ba. Mutanen unguwa kuwa da ba'a rasa ɗan adam da sa ido tuni har sun fara tsegumi da.gunaguni akanta. Sannu a hankali har magana ta fara dawowa kunnen mafiƴarta.
Wannan abu na damun mahaifiyarta tsahon lokaci. Ana haka sai aka sami wasu sabbin maƙota da su ka tare kusa da su. Wannan maƙociya ta na da wata kanwarta da aka bata ita a matsayin ƴar zaman ɗaki mai suna Hasiya. Hasiya dai za ta yi kimanin shekaru ɗaya da Mairama. Anan ne bayan sun ɗan kwana biyu mahaifiyar Mairama ta je ta nemi su ƙullawa yaran na su ƙawance. Haka nan aka yi kuwa. Mairama da Hasiya su ka zama manyan ƙawaye.
Wannan ya sauya rayuwa da halayen Dela wato Mairama daga na mace mai halin ƴan maza da kyakkyawar budurwa ƴar ƙwalisa. Tare su ka kpma yin komai daga cin abinci zuwa wasa har zuwa makaranta. Mahaifiyar Mairama ta yi matuƙar farinciki da wannan sauyi na nan taƙe da ƴar tata ta yi. Takan aika kyautuka tace a baiwa Hasiya inji Mairama suma kuma su ma aikowa da sunan Hasiya lr ce ta aikowa da Mairama. Wannan ya ƙara shaƙuwa da amintaka mai ƙarfi tsakanin su.
Ba su taɓa yin saɓani wanda har aka samu mutum na uku ya san da shi ba. Tate su ke yi wa junan su uzuri. Idan ɗaya ta ɓatawa ɗayar za ta nemi yafiyarta a wuce wajen.
Wannam ya cigaba har zuwa auren su inda su ka auri abokan juna da suka gina musu gida a unguwar Sabuwar Matan Ƙwarai da ke yamma da gari su ka zauna cikin jin daɗi da watada da ƙoshin lafiya.
Comments
Post a Comment