MAMUDA ADALUM SARKI
MAMUDA ADALIN SARKI
Sarki Mamuda wani sarki ne da aka yi shi a ƙasar Arawa mai son talakawan sa da kuma kyautata musu a iya bakin ƙoƙarinsa. Sarkin Mudi kamar yanda wasu kan taƙaita sunan sa ya kafa gagarunin tarihi a ƙasar Arawa ta yanda bayan ya yi sarauta duk wani yaro da aka raɗawa su na Mamuda to fa tabbas sunan sa ya ci. Wanna ya sanya har yanzu ƙasar cike da masu irin wannan suna bila adaɗin, kuma akn yi wa mai irin sunan ƙaƙabi da Mudi ko Mai Arawa.
Sarki ya sami wannan soyayya ne da ƙauna daga talakawan sa saboda kyawawan dabi'unsa. Duk wata ɗabi'a da za ace ma ta tur, to sarki baya ko kusantar hanyar ta tun yana saurayi ma kafin ya hau karagar mulki. Duk da kasancewar sa ɗan sarki kuma jika sarakuna ta ɓangaren uwa da uba, wannan bai sanya sbi ya lalace ba ƙamar yanda aka saba ganin masu irin matsayin sa su na zama sangartattu, taɓararru kuma marasa daraja jama'a ga girman kai da aikata wasu manyan katoɓara da yin ƙaurin suna wajen aikata baɗala.
Ya kasance duk talakawa ne yawancin aminan sa sai ƴan tsiraru daga cikin ƴan cikin gidan sarauta waɗanda yaga ta su za ta zo ɗaya. Bayan da aka yi maaa sarauta ne ya janyo waɗancan aminai na sa suka zama da shawarar su ya ke zartar da hukunci ba wai wadda miyagun fadawa ke baiwa sarakuna ba kamar yanda aka saba a baya ba. Wannan lamarin ya na baƙantawa mutanen fada amma sai dai kuma ya na farantawa jama'ar gari baki ɗaya.
Bayan da wutar hassada da gaba ta turnuƙe Galafima, sai ya shirya ganin bayan Sarki ta kowane hali. Galidiman dai ya kasance ƙani ga mahaifin Sarki mai ci. Ya daɗe ya na son karagar nan amma kuma bai samu ba sai ɗan ɗan uwansa aka naɗa ga shi kuma ya ƙi amincewa da su a matsayin manyan mashawartan sa. Da wannan gabar ya yi anfanin wajen sanyawa Sarki dafin kunamar duhu a cikin alkaki kasnacewar ya san Sarki ya na son akakin da ya nutse cikin tatattaciyar zuma.
Cikin kariyar Ubangiji Sarki zai kai alkakin bakinsa kenan sai ya ga kyanwar sa tana kallonsa kuma tana kau da kai. "Ke ma Faratu alkakin zaki ci ne?" Ya tamabayeta kamar dai yanda daman ya saba magana da dabbobin da ya ke kiwo kuma ya kan sanya musu sunaye kai kace su na jin Hausa. Bisa ga mamaki wani lokacin idan ya yi magana da su sai ka ga sun ɗaga kai ko sun girgiza kamar dai su na ƙoƙarin mayar masa da batunsa. Nan ya fara gutsurowa kyanwar ya jefa mata. Nan da nan ta cinye ta na tanɗe baki. Sai ya kuma ƙara mata wani kafin ta cinye na biyu ta faɗi ƙasa ta na shure-shure. Nan take kyanwa Faratu ta fadi matacciya akan kilishin da ke dakin Sarki.
Sarki ya kira jakadiya da babbar murya ta nufo inda ya ke cikin hanzari. "Ga ni Allah ya ƙara ma yawan rai.". Jakadiya ta amsa cikin girmamawa. Sarki ya ce: "Waye ya aiko mana da wannan alkakin?" Jakadiya da kalli mage da ke kwance baki duk dafara ta ce: "Mai girma Galafima ne ya aiko shamakinsa Allah ya ƙara maka imani." Jakaɗiya ta faɗa cikin rawar jiki da kyarmar murya.
Sarki ya yi unarni da azo masa da Galadima. Tun da Galadima ya hango dogarai ba takalama da bulalai da gorori ran su a ɓace cikin fushi, ya san cewa shirin sa ya ɓaci. A lokacin da su ka isa gare shi ba ko gaisuwa su ka tankaɗo ƙeyarsa sai gaban Sarki. Wannan abu ya yi wa Galadima zafi da ƙunci. Wai dogarai ne su ke yi masa wannan tozarcin? Da aka je gaban Sarki sai su ka dankufar da shi ta karfin tsiya a gaba Sarki. Sarki ya ce a basu waje zai tattauna da Baffansa su kaɗai. Sarki ya tambaye shi me yasa ya ke son rayuwarsa Galadima ya yi shiru ya na taɓa ƙugunsa ashe wata rantsattiyar wuƙa ya ke shirin ɗaukowa. Ya na zarota kuwa ya dabawa sarki a kuiɓinsa. Sarki ya rafka salati sai ga dogarai cikin.hanzari, su ka yi kan Galadima. Sarki ya dskatar da su ya ce a kira masa sarkin wanzamai.
Aka tafi da Galadima aka kulle sarkin wanzamai ya baiwa Sarki maganin karfe da na dafin da aka sanya a jikin wukar da aka soke shi, aka ɗaure wajen da kyalle bayan an sanya magani akan wajen kafin a ɗaure. Sannan ya ba da maganin sha da ruwa da kuma na yin salala. Kafin mako guda zurfin ramin da aka daɓawa Sarki wuƙa ya fara cikowa kuma Sarki ya fara samun lafiya. Hankalin talakawan garin ya yi matuƙar ta shi ganin cewa sarkin su mai ƙaunar su na kan gadon mutuwa. Sun je har gidan yari inda su ka ɓallo Galadima ta ƙarfi su ka dinga duka da suka da wuƙaƙe da duka da sanduna da gorori har sai da su ka ga ya daina motsi.
Lokacin da Sarki ya samu labarin mutuwar Galadima ya yi matuƙar baƙin ciki kuma bai ji daɗin ɗanyen hukuncin da jama'ar gari su ka yanke cikin fushi ba. Bayan sati biyu da faruwar hakan ne Sarki ya sanya aka nemo duk magoya bayan Galadima a fada aka kore su daga gari. Yace: "Daman na yi niyyar aikata hakan ga marigayi Galadima da masu taimaka masa a fada da zarar na samu lafiya. Amma sai ga shi wasu sun hallaka shi" Sarkin ya faɗa cikin wata irin murya mai cike da alhini.
"Ni ba na son cutar da kowa ko da kuwa wanda ya yi yunƙurin kashe ni ne!" Sarkin ya ƙarasa maganarsa kamar ya ƴi kuka. Mutanen garin su ka ce: "Allah ya karawa Sarki lafiya!" da wata irin babbar murya guda ɗaya.
Wani daga cikin su mai garjin murya ya ce: "Allah ya taimaki sarki sai an sanya ido fa a kansu. Saboda mun san tausayinka da afuwarka shi ya sa mu ka gama da babban na su domin da an kore shi, to da ya je ya haɗa kai da magautan Arawa ya zo kuma ya tarwatsa kowa da komai ɗaga baya" Nan kuwa waje ya ruɗe da sowa kowa sai cewa ya ke: "Wannan gaskiya ne wannan gaskiya ne!"
Sarki ya cigaba da mulkin sa cikin adalci da ƙauna da shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsa da talakawan sa. Bayan rasuwarsa ne kuma aka naɗa ɗan Mamuda na huɗu wanda shi ne ɗan autan sa wanda kuma ya kasance ɗa namiji guda ɗaya tilo. Shi ma ya yi mulki irin salon mahaifinsa kai harda ma ƙari cikin walwala da son talakawan sa.
Comments
Post a Comment