RIJIYAR DUDDURU DA TA AFKAU

RIJIYAR DUDDURU DA TA AFKAU

Ga ta nan ga ta nan ku!

An yi wata kyakkyawar yarinya marainiya mai suna Tamasu a garin Yalwan Tumbau. Ta na da shekaru bakwai ne mahaigiƴarta ta rasu. Kafin rasuwar mahaifiyarta sai da ta yi mata wasiƴya da cewa duk abinda za ta aikata ta fara zuwa wajen wata bishiƴar tsamiya ta tambayeta tukuna 

Mahaifiƴar yarinyar nan ta ma da kishiya mai wani irin baƙin kishi. Tunda aka auro mata marigayiyar a matsayin kishiya ta sanya mata karan tsana. Ta kasance ta na da ƴaƴa mata guda biyu sangartattu. Kai lokacin da mahaifiyar Tamasu ta haifeta ko barƙa ma ba ta iya yi mata ba duk da tsananin wahalar da ta sha a wajen naƙuda.

A na nan ana nan har Tamasu ta fara iya rarrafe. Idan ta rarrafa wajen ɗakin kishiyar mahaifiyar tata sai kawai a jiyo ta tsandara kuka. Wata rana uwar ce ke muntsininta ko mugun kallo mai tazana yara, wata rana kuma ƴaƴan na ta ne su ke yi wa Tamasu mugunta da ƙeta iri-iri. 
 A lokacin da mahaifiyar Tamasu ta fuskanci abinda ke faruwa sai su ka dinga zama a.ɗaka daga ita sai ƴar ta ƴar ƙarama.
Duk wannan halin da su ke ciki  mahaifiyar Tamasu bata taɓa ɗaga kai ta kalli kishiyarta da wani mummunan abu ba, kainhatta maingidan su ma baiɓsan halin da sunke ciki ba sai daga baya ya fara fuskanta. Ko da ya ke ma matar taɓsa dai tafi ƙarfinsa domin kuwa ko faɗa baya iya yi wa sangartattun ƴaƴanta a gabanta.

Haka yarinya Tamasu da mahaifiyarya su ka zauna cikin tsangwama da takura. Kullum su na ɗaki ba damar fitowa ko tsakar gida saboda bala'in kishiƴa da ƴaƴanta biyu. Tsangwamar yau daban ta gobe daban duk da cewa ba sa fitowa. Wasu lokutan har ƙawayensu da sauran futsararrun yara su ke gayyatowa na maƙofta domin taruwa su dinga yin jifa zuwa ɗakin mahaifiyar Tamasu.

Bayan rasuwar mahaifiyar Tamasu ne fa abubuwa su ka ƙara ta'azzara a gareta. Duk wani aikin gida ita ce ake ɗorawa ko da kuwa ƙarfinta bai kai ta yi shi ba. Kullum sai an turata ɗiɓar ruwa tsakar dare a rijiyar Afkau mai tsananin zurfi da kwazazzabai ga kuma ƙwanƙwamai duk a cikinta.

Duk sanda aka tura ta ɗebo ruwa rijiyar Afkau sai ta fara zuwa wajen bishiƴar tsamiyar nan da ake ce ta dinga yin shawara da ita ta tambayeta cikin rera wata irin waƙa mai daɗi da sanyayyar muryarta mai ɗaukar hankali ta na cewa:

Tsamiya tsamiya wajen ki na zo
Na je ni Dudduru ko na je Afkau?
Na je ni Dudduru ko na je Afkau?

Sai ita kuma tsamiyar ta ce:

Je ki Dudduru kar ki je Afkau
Afkau kisa ta ke za ta afka ki
Jeki Dudduru kar ki je Afkau
Afkau kisa ta ke za ta afka ki!"

Shi kenan yarinya sai ta je Dudduru ta ɗebo ruwan kuma ta dawo lafiya. Ana haka kullum ashe wannan abu ya na ƙara ɓatawa kishiyar uwarta rai saboda duk sanda ta komo daga ɗiban ruwan nan tsakar dare sai ta lakaɗa mata duka ta na cewa: "Ba Afkau ki ka je ba ko? Afkau na ce ki dinga zuwa ja'ira!" Ta na duka ta na ja mata kunne da ƙarfi da kuma ƙeta.

Kullum ana haka har wata rana yariman garin ya dawo daga farauta tsakar dare sai ya dinga jin ana rera wannan waƙar mai ɗaukar hankali daga can wajen bishiyar tsamiya. Ƴa na matsowa daɗin waƙar ya na ƙara bayyana. Sai ƴa laɓe ya ga abinda yarinyar nan ta aikata. Bayan ta je rijiyar Dudduru ta ɗebo ruwan ne, sai ya biyota a baya a baya har ya ga gidan su.

Washe gari Yarima ɗan sarki ya tashi da tawagar abokansa ƴaƴan manyan gari ya shirya hawa sai gidan su Tamasu. Ya na aikawa sai aka hana ta fita. Kishiyar mahaifiyarya ta aika babbar ƴar ta. Shi kuwa Yarima ya ce ba wannan ba ce. Bayan ya dage ne har da tura wasu fadawa cikin gidan aka lalubo masa Tamasunsa.

Ranar nan kishiyar uwarta da ƴaƴanta biyu ko runtsawa ba su ƴi saboda tsabar baƙin cikin. A wannan daren su ka aske gashin kan Tamasu tas su ka shafe kan da ta toka. Gashin Tamasu ya kasance ya na kaiwa har gadon bayanta, ga kyalli, ga baƙi ga kuma sheƙi. Tamasu ta sha kuka a wannan daren har sai da fuskarta ta kumbura.

Yayinda Yarima ya samu labari sai ya sanya aka kama wannan muguwar uwar da ƴaƴanta aka kai su gidan yari. Ita kuwa Tamasu ya aika tawaga da kyautukan ƙasaita zuwa wajen ƴan uwan mahaifinta aka nema masa aurenta. 

Bayan anyi auren ne Tamasu ta nemi alfarmar wajen Yarima cewa a sako ƴan uwanta biyu da mahaifiyar su. Bayan Yarima ya gama turjewa da ƙyar ya haƙura. Tamasu ta yi musu kyautuka na abin arziƙi su ka karɓa su na kuka kuma su na bata haƙuri da neman afuwar ta.
Ƙurunƙus ɗan kan ɓera!

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya