TSAHIRO TSAGE
TSAHIRO TSAGE
Tsahiro yaro ne mafaɗacin gaske. Duk sanda ya fita waje da riga sai ya dawo da ita a yayyage saboda tsabar dambe da shaƙa da faɗan da ya ke yawan yi har da matasan yaran da ma su ka fi shi a shekaru. Duk iyayen sa sun yi sun gaji. An yi masa addu'ar an bashi ruwan alwalar an bashi ruwan randar masallatai tara amma duk zuciyar sa bata risuna ba sai ma kara tsauri ta ke yi
Tun yana ɗan shekara biyar ne kakarsa ta sanya masa wannan suna na Tsage. Lokacin da aka tambayeta: "Wai shin menene tsage ne Kaka? Sai ta ce: "Ai tsage wani irin mafaɗacin kifi ne wanda idan su ka fara faɗa har sai ɗaya yaga ɗayan ya mutu baya ko motsi sannan faɗan zai ƙare." Wannan mummunan suna dai tabbasa ya bi Tsahiro kuma ya na tasiri akansa tunda daman ance suna linzami.
Bayan da ya cika shekarun zuwa gabas ne aka ɗauke shi daga gaban iyayen sa aka kai shi tsangayar Malam Goni Bukar Ghana da ke can Gabas. Anan ma dai mai hali bai fasa halin nasa ba. Malam sai da ya gaji da kawo ƙarar sa da ake yawan yi. Malam ya yi nasihar shi ma har ya gaji.
Wata rana bayan ya kai Malam bango sai malam ya sa aka samo ruwan Zam-zam lokacin da alhazai su ka dawo da ga aikin Hajji. Ya baiwa yara almajirai aikin rubuta Ya Halimu ya Saburu dubu sau dubu. Su na yi su na ƙirgawa su na wankewa da ruwan Zam-Zam a cikin wani babban daro. Sai da aka yi Laraba bakwai ana yin wannan aikin. Bayan da aka kammala ne Malam ya sanya aka samo akuya aka yanka aka yiwa Tsahiro aski aka raɗa masa suna Muhammadu kuma aka ce Malam ya tsine duk wanda ya ƙara kiransa da Tsage. Sannan aka ce ya yi Bismillah ya zauna ya sha ruwan nan.
Ba ayi kwana uku ba Muhammadu (sabon sunan Tsaburu Tsage) har ya gama yin laushi. Yanzu daga ya ga abu zai ɓata masa rai ma shi ne zai fara ba ka haƙuri ko kuma ya bar wajen gaba ɗaya. Haka nan ya mayar da hankali kan karatun sa. Kullum sai gaba ya ke yi har ya sami Alƙur'ani mai girma da karatu mai inganci da tilawa mai ƙwarin gaske.
Lokacin da ya koma gidan ne ya sanar da iyayen sa cewa Malam fa ya sauya masa suna yanzu Muhammadu sunan sannan kuma an tsine kiran sa da suna Tsage. Mahaifansa sun ji daɗi aka yi masa walimar sauka tare da sanar da jama'ar gari cewa yanzu sunan sa ya koma Malam Muhammadu har aka sanya Sanƙira ya zaga gari duk ya sanarwa da babbar muryar nan tasa mai karaɗe gari.
Ƙurunƙus!
Comments
Post a Comment