TUNFAFIYAR KAN SHURI
TUNFAFIYAR KAN SHURI
Wata rana da Jume da Rabe da Mahe su ka hada kai su ka tafi farautar beran daji shiyyar Kwarin Shuri. A daidai lokacin Baffan su Aminu ya hango su sun hade kai sun nufi wajen ya kirawo su ya ce da su: "Ina za ku je da tsakar ranar nan haka? Sai wannan ya kalli wancan su ka hau in'ina irin ta marasa gaskiya. Sai Rabe ya yi caraf ya ce wa Kawu: " Ai daman aiken mu aka yi mu yi wo icen girkin rana" Sai kawu ya ce to: "To Allah ya tsare, amma ba'a son shiga wajen nan fa da garjin rana haka, dafatan dai za ku kiyaye" Duk sai su ka kara hada baki su ka ce ma sa: "e za mu kula Kawu"
Bayan rabuwar su da Kawu Aminu ne duk su ka bushe da dariya su na cewa: "Amma dai Rabe ka iya shirya karya,. Wato wai itace za mu yi wo ko?" Duk su ukun su ka kara bushewa da dariya su na kara nausawa cikin sarkakiyar duhuwar bishiyoyin Kwarin Shuri. Su na cikin tafiya ne sai su ka hango wani shurin da ya ke na jar kasa zalla. Jume ya ce aje a zuzzungura sanda ko za'a samu berayan daji. Mahe ya ce kada mu je saboda an fada mana ba'a zuwa wajen shurin nan musamman ma da tsakar rana. Rabe da Jume dai ba su tsaya sun saurari Mahe ba.
Bayan tsawon lokaci su na ta zungure-zunguren sanda a cikin shuri da sauran duk wasu ramuka da su ka gani ne, sai su ka je karkashin wata bishiya su ka zauna su na hutawa. Daga nesa sai Rabe ya hango wani shuri wanda wata rikakkiyar tumfafiya ta fito akansa. Mahe ya kara jaddada musu kan cewa su hakura su koma gida tunda dai sun gaza samun berayen dajin da za su farauta. Duk sai su ka ki sauraronsa har su na ce masa zabo ne shi sarkim tsoro, idan ya san haka zai musu mai yasa ma ya biyo su farautar to? Shi dai Mahe ya je gefe ya yi zaman sa. Su kuwa su Rabe da Jume su ka nufi wannan shuri mai tumfafiya. Sun daga adda za su sare tumfafiyar nan kenan sai kawai su ka fara jin wata waka da wata irin murya mai abin tausayi ta na fitowa daga cikin shurin ta na cewa:
"Kar ka taba ni kar ku tabani
Kar ka bugeni za ku cire ni
In ka cire ni za ku kashe ni
In ka kashe ni kun cuce ni
Dangina ba za su bari ba
Dangina ba za su bari ba"
Haka nan wannan waka ta dinga fitowa daga cikin shurin nan ita kuma tumfafiyar kan shurin ta na wani rangaji kamar dai tana taka rawa ne ga wakar da ke fitowa. Amma da ke su Jume da Rabe ba sa jin magana sai da su ka sare tumfafiyar nan. Sarewar su ke da wuya kenan sai wata irin jar guguwa ta turnuke sararin samaniya ta na wata irin kara whooooooooo ta na awon gaba da duk abinda ya ke kusa da ita, a haka ne ma ta janye Jume da Rabe ta yi cikin shurin nan da su. Tun ama jin kururuwar su har aka daina jin duriyar su. Bayan guguwar nan ta hadiye matasan nan sai aka ji kurar ta lafa kuma wajen ya washe, shi kuwa Mahe ya na daga gefe sai ya dinga jin wata irin mummunar dariya mai amsa kuwwa ta na fitowa faga cikin wannan shuri daga nan kuma sai shurin ya bace ma gaba daya sai wata yar kurar da bata wuce a shareta da tsintsiya ba ce ta rage a gurbin shurin.
Mahe dai duk gwuiwowimsa sun yi sanyi saboda abubuwan al'marar da ya gani da kuma wadanda ya ji. Da kyar dai ya samu ya koma gida cikin dimuwa, damuwa da gajiya. Mahe ya kwashe labarin duk abunuwan da su ka faru ya fadawa iyaye da yan uwans su Rabe da Jume. Tun daga wanna ranar ne aka hana shiga Kwarin Shuri ga dukkan yara don gudun kada su je su tsokano mutanen boye da ake zaman amana da su.
Kurunkus!
Comments
Post a Comment