IYAMMU
IYAMMU Hajiƴa Iyammu wata tsohuwa ce wadda ke da kyakkyawar zuciyar rainon yara mata marayu kuma tsayawa akan karatun su da tarbiyyar su. Ta raini yara masu tarin yawa kuma har zuwa kayan ɗaki da gara ta ke yi musu idan an ta shi aurar da su. Saboda shekarunta ne kowa ya ke kiranta Hajiya Iyammu. Ta kan shiga lamarin duk wasu waɗanda ta fuskanci suna cikin buƙata a gidajen maƙobta da ma waɗanda ta samu labarin su waɗanda ke nesa da ita. Allah mai ikonsa duk gwagwarmayar rayuwa da aure auren da ta yi Allah bai nufa zata samu ɗa ba ballantana ma jika a rayuwarta. Wannan ya sanya ta cigaba da ayyukan alheri da duk dukiyar da ta mallaka domin kuwa idan ta bar su ma ba ta wani tartibin magaji sai dai a dangin dangiro na can nesa. Tun lokacin da ta ke da jininta a jika ta ke harkar safara zuwa ƙasashen Kurmi. A can ne ta ke saro murjani da sauran duwatsun da ake samowa daga teku ta kawo su nan Arewa domin sayarwa ga ƴan kasuwar shinku da ke neman su ruwa a jallo saboda manyan sarakuma da att...