KASSU ATTAJIRI

KASSU ATTAJIRI

A can garin Ƙauran Namanzo anyi wani babban attajiri mai suna Kassu, wanda ya mallaki dukiyar da ko shi kan sa ma bai san yawanta ba. Ana kiransa da Kassu ne saboda an haife shi ranar da kasuwa ke ci a garinsu.

Wasu jama'a na zargin cewa wannnan dukiyar ta sa wai ta samo asali ne daga aljanu. Wai ana cewa wata aljana ya taɓa taikawa shi ne ita ma ta ci alwashin cewa sai ta saka masa kuma ta dinga taimaka masa wajen samun buɗi ta ko ina. Wasu kuwa su ka ce wai wani malaminsa ya taɓa yi wa wata bajinta shi ne shi kuma malamin ya roƙa masa arziƙi da shuhura a duniya. To koma dai wannene daga ciki haƙiƙa Kasuu ya gawurta ta yanda har yau har kwanan gobe an rasa wanda zai iya kawowa ko kusa da inda ƴaƴan jikokinsa su ke tashen kuɗi a halin yanzu a faɗin ƙasar ma baki ɗaya.

A lokacin da yake raye, Kassu ya taimakwa talaƙwa da dama su ma har sai da su ka zama manyan attajirai. Idan ya fitar da zakkarsa ra sgekara ya kan nemi talaka tiƙos amma wanda ya ne fafutuka a wata harka amma ba gaba ba baya sai ya sanya a bashi kuma ya riƙo hannunsa ya ɗora akam harkokin da zai.cigaba da bunƙasa wannan dukiyar. Sakamakon wannna alheri da yayi ne ya sanya fiye da rabin masu arziƙi a wannan ƙasar ta mu yanzu ko dai su zama jikokin ƴaƴansa na cikinsa ko ƴaƴan jikoki ko kuma su zama ƴaƴan jikokin mutanen da ya taɓa tallafawa a baya.

Saboda tsabar  dafaffen abincin sadaka da ake yi a gidan sa, idan aka ɗora tukunyar koko tun kafin Assalatu, to ba za'a sauke ba sai lokacin keanciyar barci yayi domin kuwa yini ake yi sinkir ana ta dafedafen abinci nau'i nau'i domin rarrabawa ga talakawa mabuƙatan da ke tutruruwa a ƙofar gidan domin jiƙa maƙoshin su. Babu wanda ya ke kwana da yunwa a lokacin rayuwarsa saboda shi wanmam attijiri ya yi imanin cewa wannan tarin dukiyar sam ba ta sa bace ahi kaɗai. Allah ne kawai ya damƙa masa wannan babban rabon domin ya gwada shi kan ko zai iya yim alheri ko kuma zai dinga yin daga ƙwauri sai gwiwa?

A lokacin da ya bar duniya hatta dabbobin da ya ke kiwo kamar su kyanwoyi da dawaki duk sai da aka ga su na ta zubar da hawaye shaɓe-shaɓe.

Anan sai Iya ta ƙare tatsuniyarta da cewa: "Anfanin arziƙi shi ne mutane da dama su samu damar da za su anfana da shi."

Comments

Popular posts from this blog

JUMMAI KUNYA

ƳAR BORA DA KIFANYA

Saƙa Da Zare Ɗaya