MALAM MAI DARA
MLAAM.MAI DARA
Wata rana wani maharbi ya shiga jeji da bakar sa rataye a kafaɗa domin farauta. Ya sanya bunjuma taɓfarin saƙi da jar dara akan sa sanann kuma ya na goye da kibau a bayan sa. Bayan ya gama zagaya daji bai samu wani abinda zai iƴa farautowa ba sai ya hangi wata ƴar ƙaramar tsuntsuwa a kan bishiya.
Sai ya ce a ra sa " Bari na harbo tsuntsuwar nan ko.ɗan gasawa nayi na ci da dare." Bayan ya gama auna ƴar tsuntsuwa zai harba sai ya ji ta na yin wata waƙa ta na cewa:
Aauna ni a hankali
Malam mai Dara
Kar ka je ka yi rauni
Malam mai Dara"
Sai da ya gama auna ta sarai sai dai ya sake jin ta na cewa:
"Hahharbo ni a hankali
Malam mai dara
Kar kaje ka yi rauni
Malam mai Dara"
Yayimda ya ƙara kasa kunne sosai sai dai ya ji cewa tabbas da shi wannan ƴar tsuntsuwar nan ta ke yin wannan waƙar tata ba wai jin kunne ya yi ba. Har ya yi kamar ya fasa harbinta ya dawo gida abin sa, sai wata zuciyar kuma ta ce masa "Kai wane irin hatsabibin kwaro ne ma baka taɓa harbowa ba ballanta wannan ƴar ƙaramar ƙaruwar? Kai fa ɗan gaɗo ne gaba da baya ba wai ɗan haye ba!" Nan take kuwa sai maharbi ya biyewa wasiƙar da zuciyar sa ta dinga aika masa sai ya harbo ƴar fsuntsuwa nan a fusace.
Ya na zuwa zai ɗauke ta bayan ta faɗo kasa sai ya kuma jin ta na yin waƙa ta na cewa:
"Ɗaɗɗauke ni a hankali
Malam mai Dara
Kar ka je ka yi rauni
Malam.mai Dara"
Ya sunkuya ya ɗauka ya sanya a jaka ya tawo gida. Bayan da ya zo zai fige ta sai ya kuma jin ta na waƙa ta na cewa:
"Fiffige ni a ha kali
Malam mai Dara
Kar ka je ka yi rauni
Malam mai Dara"
Sai maharbi ya figeta. Hakan nan ma da ya zo zai feɗe cikin da kuma yayyankata da sassoyawa duk sai da ƴar fsuntsuwa da yi masa wannan waƙar. Bayan ya gama suya sai ƙamshin nama ne ya ke tashi sai ya ɗauko yajin daddawa ya ajiye a gefe ya zauna zaman harɗe ya ɗauki tsoka guda ɗaya zai jefa a bakin sa sai kuwa ya kuma jin tsuntsuwa ta na cewa:
"Ciccinye ni a hankali
Malam mai Dara
Kar ka je ka yi rauni
Malam mai Dara"
Sai kuwa maharbin ya yi wani dogon tsaki ya u
kuma jefa tsokar tsokar ƙirjin ƴar tsuntsuwa bayan ya ɗangwalo yajin sa na daddawa. Bayan da naman ya isa uwar hanjinsa sai ya cigaba da ci ya na wani karkaɗa kafa har ya dai ƙare tas. Ya kora da ruwa ya yi gyatsa.
Bayan wani ɗan karamin lokaci kawai sai aka ga cikin maharbi nan ya na kumbura ya na kara ɗagawa. Abin al'ajabi kafin a ɗau wani lokaci cikin maharbi ya yi tsantsar kamar randa haka nan ya yi ta murƙususu har cikin ya yi wata ƙara tussh ya fashe sai kuwa ƴar tsuntsunwa ta tashi daga cikin maharbin nan ta yi sama ta koma daji ta cigaba da rayuwa abinta daman ashe ta iska ce.
Ƙurunƙus!
Comments
Post a Comment