KALELE BARBAƊIN TUSA
KALELE BARBAƊEN TUSA Ga ta nan ga ta nan ku! Akwai wani yaro mai wata mummunan al'ada ta sakin tusa a cikin jama'a ba kan gado mai suna Kalele. Ya kasance ya na aikata wannan abu tun ya na ƙarami. Wasu lokutan idan aka zauna da shi har sai ya kumburawa duk waɗanda ke wannan wajen cikin da warin tusar nan da ya ke gunsurawa. A lokacin da yara ƴan uwan sa su ka fuskanci ya na illata su, sai duk aka daina zama a inda ya ke ko kuma da zarar shi ya zo cikin yara ya zauna, duk sai kowa ya watse. Wannan abin ya na damunsa amma ya rasa mafita. Ana haka har ya zama saurayi. Duk sauran tsaraikunsa sun samu ƴan mata har magana ta kai ga manya ana shirye shiryen aure, amma shi duk wajen yarinyar da ya je sau ɗaya ba ta yarda da ƙara fitowa ta biyu saboda yanda ya ke sakin abar ta sa ba kan gado kafin su gama taɗi. Ana cikin wannan hali ne sai aka yi wani baƙon wamzami mai bayar da mugunguna. Ya cire kunyarsa ya je ya yi wa wanzami bayani dalla-dalla. Sai wanzam ya ce da shi ga wasu magu...